Katsina City News
Sojan Sama, sunyi awon gaba da shugaban KASROMA na Jahar Katsina Injiniya Surajo Yazid Abukur.
Ganau ya tabbatar ma da jaridunmu cewa sojan sunyi irin aikin nan ne na kama Manyan Masu laifi. Inda sukayi ma injiniyan Dirar Mikiya a wajen cin Abincin dake filin saukar Jiragen sama na Umaru Musa yar adua dake katsina.
Ganau suka ce, sojan sun iske shi wajen cin Abincin yana cin abinci, suka Sanya masa hular nan baka ta rufe fuska, suka bankare shi ta baya, suka Sanya masa ankwa.
Nan take sojan sukayi awon gaba dashi cikin matakan tsaro, zuwa yanzu babu Wanda ya San ina ne,har zuwa hada wannan rahoton, babu wani bayani daga wajen Sojojin.
Mun tuntubi kakakin rundunar yan sanda na jahar katsina, yace basu da masaniya akan maganar.
Duk makusantan Surajo Yazid Abukur sun ki cewa kala akan lamarin.
Binciken mu ya tabbatar mana, sojan sama suna da bin kaida da Doka a wajen tafiyar da Aikin su.
Don haka dalilin da zai Sanya ayi ma Injiniya Surajo Yazid Abukur wannan dirar mikiya a wajen cin abinci, kuma a filin jirgin sama abin tambaya ne.