• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Sashen Hausa

Sifeto-Janar ya soke kawo CP Olaleye, ya aiko Kontagora a matsayin sabon Kwamishinan Ƴansanda zuwa Kano

Katsina City News by Katsina City News
March 14, 2023
in Sashen Hausa
0
Sifeto-Janar ya soke kawo CP Olaleye, ya aiko Kontagora a matsayin sabon Kwamishinan Ƴansanda zuwa Kano
0
SHARES
14
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Sufeto Janar, IGP Alkali Baba ya soke turo da Feleye Olaleye a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sanda a Kano.

A don haka, IGP din ya aiko CP Ahmed Kontagora ya jagoranci rundunar a lokacin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha a jihar.

A ranar 8 ga Maris, IGP ya sauya matakin da ya dauka na tura CP Balarabe Sule, tsohon babban jami’in tsaro na gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, biyo bayan zanga-zangar da aka yi a kan hakan.

Amma a wata sigina da aka fitar ranar Litinin mai lamba TH.5361/FS/FHQ/ABJ/SUB.6/144, IGP din ya ci gaba da tura CP Ita Lazarus Uko-Udom zuwa Kano ta Tsakiya, inda DCP Umar Iya ya zama mataimakin sa.

Yanzu haka dai IGP din ya mayar da CP Faleye Olaleye daga jihar Ebonyi zuwa Kano domin ya jagoranci rundunar a lokacin zabe.

Jam’iyyar adawa ta NNPP ta gudanar da zanga-zanga bayan rahoton DAILY NIGERIAN na cewa za a turo mutane uku, CP Balarabe Sule, ACP Adamu Babayo da ACP Abubakar Shika zuwa jihar Kano

A cewar masu lura da al’amura, ‘yan sandan uku, wadanda suka taba yin aiki tare a jihar, ana kyautata zaton jami’an bangaranci ne da ake amfani da su a matsayin jami’an murkushe ‘yan adawa.

DAILY NIGERIAN dai ta tattaro cewa zanga-zangar ta yi tasiri ga IGP ɗin inda ya fasa aiko CP Sule ɗin.

IGP din ya kuma sake tura karin wasu manyan jami’ai zuwa jihar domin karfafa tsaro a lokacin zabe.

Kamar yadda jaridar DAILY NIGERIAN ta gani na baya-bayan nan, IGP din ya tura AIG Sani Dalijan domin ya jagoranci shiyya ta daya a Kano.

Haka kuma takardar ta nuna cewa Ita Lazarus Uko-Udom ne zai jagoranci Kano ta tsakiya, inda DCP Umar Iya zai kasance na biyu a matsayin shugaba.

Alkali ya kuma aike da DCP Abdulkadir El-Jamel domin kula da kananan hukumomin Albasu, Gaya, Rogo, Takai, Ajingi, Garko, Wudil da Sumaila.

A kananan hukumomin Rano, Bebeji, Bunkure, Doguwa, Kiru, Kibiya Tudunwada dake jihar Kano ta kudu kuwa, IGP ya tura DCP Adamu Ngojin domin ya kula da tsaron a can haka.

IGP din ya kuma tura DCP Abaniwonda Olufemi zuwa Kano ta Arewa, tare da ACP Adamu Sambo a matsayin babban kwamandan sa na biyu.

Kamar yadda sabuwar takardar ta nuna, DCP Auwal Musa ne zai jagoranci CID, yayin da DCP Aminu Maiwada zai dauki nauyin gudanar da ayyuka a hukumar ta Kano a lokacin zabe.

Share

Related

Source: Daily Nigeria
Via: Katsina City News
Previous Post

CBN ya ce a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudi

Next Post

Tinubu consoles Kano traders over market fire

Next Post
Tinubu consoles Kano traders over market fire

Tinubu consoles Kano traders over market fire

Recent Posts

  • Hajj 2023: Azman begins airlift of pilgrims Today
  • Hajj Airlift: NAHCON Airlift 14,000 pilgrims in 33 flights operations, set up back up plans
  • Hajj 2023: Plateau pilgrims “stranded’ over “failure to remit funds” for Hajj officials
  • Abin da aka tattauna a taron Tinubu da gwamnonin Jam’iyyar APC
  • Makkah service providers pledges ‘memorable’ Hajj 2023 for Nigerian pilgrims

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • June 2023
  • May 2023
  • April 2023
  • March 2023
  • February 2023
  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Interview
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Press Release
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Sashin Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Interview
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Press Release
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Sashin Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.