….. Sunyi alkawalin goyon bayan duk yan takarar jam,iyyar APC.
Shuwagabannin Fulani wato (Ardo) daga sassa daban daban na Najeriya sun jaddada goyon bayansu ga dan takarar jam,iyyar APC Senator Bola Ahmed Tinubu a wani taro da suka gudanar a babban birnin tarayya Abuja a ranar lahadi.
A taronda sukayi tareda hadin kan kungiyar sabuwar Arewa wato “Arewa New Agenda” shuwagabannin sunyi alkawalin yin amfani da yayan kungiyar 33,661 wajen janyo kan sauran yan uwansu Fulani domin su zabi Sanata Bola Tinubu.
A lokacinda yake nashi jawabi bayan an kammala al,adar Fulani ta rabon goro ga mahalatta taron shugaban kungiyar Aliyu Liman Bobboi yace raba goron da akayi yana nufin shuwagabannin zasu koma gida su isarda sakon shawararda aka yanke a wajen taron zuwa ga mabiyansu.
Yace kara da cewa taron an gudanarda shi ne domin su nunawa duniya goyon bayansu ga Tinubu saboda sun yarda sun kuma yi amanna da cancantarsa suna kuma masu adduar samun nasara a zabe mai zuwa.
Ya kara da cewa Ardo a matsayinsu na shuwagabanni suna da ta cewa sosai akan Wanda mutanensu zasu zaba, kuma suna da yakinin cewa magoya bayan nasu zasuyi masu biyayya.
Liman yayi nuni da makusanta shakikai dake tareda Tinubu kamar Gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje, Abubakar Badaru na jigawa, tsohon shugaban EFCC Malam Nuhu Ribadu, da sauran manyan Fulani yace wannan na nuni ga yadda Tinubu ya dauki kabilar ta Fulani da muhimmanci.
Kungiyar ta shuwagabannin Fulani ta kuma bawa Tinubu sarautar Barkindo.
Gwamnan jahar kano Abdullahi Umar Ganduje da yake bayani yayi tsokaci akan irin bajinta kwarewa da kuma cabcantar Tinubu da ya shugabanci Najeriya. Ya kuma kara da cewa Fulani a matsayinsu na kabila fake fuskantar barazana a sassa dabban dabban suna bukatar zabar shugaban da zai iya basu kariya.
Ganduje ya kara da cewa suna nan kan kokarin samarwa Fulani da wani tsari Wanda zai bunkasa hanyoyin kiyo a duk fadin kasar nan.
A nasa bayani dan takarar shugaban kasa na jam, iyyar APC Senator Tinubu yayi tsokaci akan irin kyakkyawar alakar da ke tsakaninsa da mahaifiyarsa a bangare daya da kuma Fulani a dayan bangaren. Ya nuna cewa alakarsa da Fulani amana ce ka alaka ce da ta kasance ta dindindin.
Ya kara jaddada niyarsa ta samarwa Fulani hanyoyin kiyo na zamani da zasu kawo ci gaba da kuma yalwa ba tareda tsangwama ba.
Tinubu kara da cewa bai taba tsammanin zai hadu da bafulataninda yafishi jin yaren yarbanci ba sai gashi yau ba zato ba tsammani ya hadu dasu. Yace wannan abun a yaba ne.
“Wannan itace irin Najeriyarda muke bukata, kasa daya al,umma daya. Ina mai tabbatar maku idan da zamu kasance anan tsawon sa,o,I biyar iyakacindai zancenda zakucigaba da ji daga gareni kenan. Ina mai matukar mika godiya da gareku.
Tabbas makiyayan Najeriya na fama da matsaloli dabban dabban amma ina mai tabbatar maku da cewa munada tsari na musamman da zai magance wudannan matsalolin.
A nashi jawabin Mallam Nuhu Ribadu ya bayyana Tinubu a matsayinsu mutuminda ya cancanta ya dace Wanda kuma zai iya kawo ci gaba mai dorewa ga kabilar ta Fulani. Ya kumayi godiya ga goyon bayanda suka bashi tareda alkawalin bazai basu kunya ba.
Ofishin yada labarai na Tinubu
Abdulaziz Abdulaziz
February 13, 2023.