• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Friday, March 31, 2023
  • Login
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Sashen Hausa

Shugaba Buhari Yasha Yabo A Wajen Shugabannin Afirka A Nijar.

November 25, 2022
in Sashen Hausa
0
Shugaba Buhari Yasha Yabo A Wajen Shugabannin Afirka A Nijar.
0
SHARES
11
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

A yau Juma’a ne ake buɗe taron shugabannin ƙasashen Afirka kan hanyar samar da masana’antu da faɗaɗa hanyoyin inganta tattalin arziƙi, a jamhuriyar Nijar.

Sai dai gabanin taron, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da wata hanya mai tsawon kilomita 3.8, a Yamai, babban birnin ƙasar, wadda aka sanya wa sunansa.

Haka nan kuma an yi wani bukin na ƙaddamar da fassarar littafi a kan salon shugabancin Muhammadu Buhari, zuwa harshen Faransanci, wanda Farfesa John Paden na jami’ar Mason University da ke Virgina ta ƙasar Amurka ya wallafa.

Wata sanarwa da fadar shugaban Najeriyar ta fitar ta hannun mai taimaka wa shugaban ƙasar kan yaɗa labaru, Garba Shehu, ta ce Shugaba Buhari ya sha yabo a bakunan shugabannin ƙasashen da suka yi jawabi.

Shugaban jamhuriyar Nijar Mohammed Bazoum ya bayyana Muhammadu Buhari a matsayin “tsayyayen mutum, maras tsoro, mai ƙanƙan da kai, riƙakken ɗan kishin ƙasa kuma masoyin mulkin demokraɗiyya.”

Ya ƙara da cewa “dagewarsa wurin yaƙi da rashawa da tabbatar da kyakkyawan shugabanci, ta sanya ƙaunarsa a zukatan kowa da kowa, yin aiki da mutum mai zurfin tunani irin shi, abin alfahari ne.”

Shi kuwa shugaban Guinea-Bissau, kuma shugaban ECOWAS, Umaro Sissoco Embalo, ya ce ya zama shugaban Guinea ne tare da taimakon Allah da taimakon Shugaba Buhari.

A cewarsa “shekara guda da ta gabata muka raɗa wa wata hanya sunan Shugaba Buhari. Baba, kamar yadda nake kiran shi mutum ne abin koyi, wanda yake a shirye wurin samar da mafita a kowane lokaci.”

A nasa ɓangaren shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby, kamar yadda sanarwar ta ruwaito cewa ya yi “Babu ko shakka Shugaba Buhari jigo ne, wanda ayyukansa da rawar da yake takawa suka sanya duniya take jin maganar nahiyar Afirka.

“Yana bayar da gudumawa wajen ci gaban Afirka ta hanyar kare nahiyar da kuma al’ummarta. Ka koya mana juri

Share

Related

Source: Katsina City News
Via: Katsina City News
Previous Post

Hukumar Ilimi ta kimiyya da fasaha a Katsina ta shirya rangadi a makarantun jihar

Next Post

Doka Ta Hana Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Kashe Sama Da Naira Biliyan 500, Cewar INEC

Next Post
Doka Ta Hana Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Kashe Sama Da Naira Biliyan 500, Cewar INEC

Doka Ta Hana Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Kashe Sama Da Naira Biliyan 500, Cewar INEC

Recent Posts

  • On birthday, clerics pray for Tinubu, Nigeria in Abuja
  • Gwamna Masari ya Kaddamar da Kwamitin Miƙa Mulki ga sabuwar Gwamnati
  • Masari: Tinubu Na Bukatar Addu’a
  • Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Karu Zuwa N46.25tr —DMO
  • FEC Approves N59.78bn For Ogoni Cleanup Projects

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • March 2023
  • February 2023
  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In