Shuba Muhammadu Buhari ya kira wannan Ambaliyar ta ruwa a matsayin wani Ibtila’i da yashafi dukkanin fadin Najeriya.
Buhari ya bayyana haka ne ta bakin wakilin sa kuma karamin ministan Ayyuka na kasa Alhaji Ibrahim El,yaqub da tawagar sa suka ziyarci kasuwar a madadin shugaban kasa.
Shugaban ya bayyana Ambaliyar ruwan a matsayin abin tada hankali da firgici. Yace Gwamnatin tarayya ta damu matuka a yayin wancen Ibtila’i, sana yayi Addu’a da fatan Allah ya kare afkuwar irin wannan abu. Ministan yayi fatan ‘yan Kasuwar zasu kaucewa gine-gine akan hanyoyin ruwa, don ganin irin wannan Ibtila’i bai sake faruwa ba. A karshe Elyaqub ya bata tabbacin cewa Gwamnatin tarayya zata iya kokarinta ta don ganin ta tallafawa ‘yan kasuwar.
A nasa jawabin shugaban masu ruwa da tsaki na kasuwar Kantin kwari Alhaji Ibrahim Haruna ya yabawa Shugaba Buhari bisa yanda ya nuna damu akan wannan Ibtila’i da ‘yan Kasuwar suka tsinci kansu a ciki, sannan yayi kira ga Gwamnatin tarayya da ta samar masu tankunan ruwa mai sola da ababen kashe gobara, a karshe yayi fatan gwamnatoci zasu ci gaba da tallafawa kasuwar da ababen bukata domin cigaban kasar baki daya