Ma’aikatar agaji da ci gaban al’umma ta tarayya ta ce sama da mutane 6000 ne suka ci gajiyar shirin nan na ci gaba da kasuwanci da karfafawar gwamnati (GEEP) a jihar Kano.
Babban sakataren a ma’aikatar Nasiru Sani Gwarzo ne ya bayyana haka ranar Juma’a a Kano, yayin kaddamar da shirin a hukumance.
Ya hori waɗanda su ka ci gajiyar da su yi amfani da ƙarfin gwiwa ta hanyar da ta dace.
Ya ƙara da cewa hakan wata dama ce ta “hawa matakin samun tattalin arziki mai ƙarfi.”
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Kowanne daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin ya samu tallafin kudi na Naira dubu 50.
Source:
Daily Nigerian