Hon. Alhassan Ado Doguwa ɗan Majalisa ne da ake zargin sa da laifin kisan kai (Culpable Homicide Punishable with Death) Kuma wannan laifin yana cikin manyan Laifuka wato Capital offences Waɗanda ba’a bada belin mutum idan ana zargin sa da aikata irin su, saboda idan har laifin ya tabbata to hukuncin sa hukuncin kisa ne a ƙarƙashin Sashi na 221 na Kundin Dokokin Manyan Laifuka (Penal Code).
Tun bayan da aka sanar da kama shi tare da aikewa dashi gidan gyaran hali, akwai Zarge-zargen da al’umma da dama suke ta yi akan cewa anaita ƙoƙarin nemar masa hanyar da za ayi amfani da ita a sake shi a idon doka, wasu suna ganin ai babu wata hanya, amma waɗanda suka san dokokin Nigeria sun san Indai gwamnatin taga damar sakin sa to tana da hanyar yin hakan dogaro da wani term a law da ake cema “Power of Nolle Prosequi”
To me ake nufi da Power of Nolle Prosequi ?
Kamar yadda yazo a Sashi na 211(a)(b) na Kundin tsarin Mulki, da Sashi na 121 na Kano State Administration of Criminal Justice Law, 2019, Shine, Attorney General (Wato babban Mai Shari’a na jiha) yana da hurumin ya shigar da ƙarar duk wanda ake zargi da aikata manyan Laifuka (kamar kisan kai) ko kuma yayi taking over ɗin ƙarar ya cigaba da yin ta, duba Shari’ar da akayi tsakanin Amaefule v. The State (1988) 2 NWLR pt. 75 156.
Kazalika, Sashi na 211(c) na Constitution ya bawa Babban Mai Shari’a na jiha hurumin ya dakatar da duk wata Shari’ar laifi da akeyi a jihar tasa (ko da dalili ko babu dalili) kamar yadda yazo a wata Shari’a da akayi tsakanin State v. Ilori (1983) 2 SC 155, to wannan dakatar da Shari’ar da Attorney General zai yi shi ake kira da “Power of Nolle Prosequi” kamar yadda yazo a Sashi na 73 da 74 na Criminal Procedure Act, da kuma Sashi na 253 na Criminal Procedure Code.
Don haka, Attorney General Yana da hurumin da zai dakatar da kowace irin Shari’a ce ta laifi, abinda zai yi kawai shine, zaije ya sanar da kotu ne (da baki ba sai yayi a rubuce ba) cewa ya dakatar da wannan Shari’ar da ake yima wane, kazalika zai iya wakilta wani yaje ya dakatar da Shari’ar a madadin sa, kamar Police Officer, ko kuma Director of Public Prosecution (DPP) amma anan dole su sai ya basu a rubuce, duba Shari’ar da akayi tsakanin The State v. Chukwura (1964) NMLR 74
To saboda haka, da zarar Attorney General yayi amfani da wannan Power ɗin ya dakatar da Shariar, to Kai tsaye za’a sallami wanda ake zargin ko ake yima Shari’ar matuƙar dai ba’a yanke masa hukunci ba, kuma Sannan nan gaba ba za’a sake kama shi akan wannan laifin ba, duba Sashi na 73(1)(2), 74(4) na Criminal Procedure Act, da Sashi na 253(3) na Criminal Procedure Code, da kuma Shari’ar da akayi tsakanin Clarke v. Attorney General of Lagos (1986) 1 QLRN 119 da Wacce akayi tsakanin Attorney General of Kaduna State v. Hassan (1985) 2 NWLR (pt 8) 483.
Shi kuma Kashi na 12 (Part 12) Sashi na 124 na Kano State Administration of Criminal Justice Law, 2019 cewa yayi, “Babban mai Shari’a na Jihar (Wato Attorney General) yana da hurumin ya dakatar da kowace irin Shari’ar laifi da akeyi a jihar tashi, ta hanyar amfani da Power of Nolle Prosequi, duk lokacin da yayi amfani da wannan Power ɗin to dole ne a sallami wanda ake yima Shari’ar kai tsaye ba tare da wani Sharaɗi ba, idan kuma an bada belin sa ne to Shikenan ba za’a sake kama shi ba, idan kuma yana tsare ne a gidan Kaso lallai ne a sake shi nan take, Saboda haka alƙalin zai rubuta ma Shugaban gidan gyaran halin takarda cewa a sake shi, kamar yadda kundin dokar Gudanar da Shari’ar manyan Laifuka na jihar Kano na Shekarar 2019 ya bayyana”
Saboda haka, Indai gwamnati taga dama tana da hanyoyin da zata sake shi ba tare da yin Shari’ar ba bare ma ayi masa hukunci idan laifin ya tabbata, idan kuma har tayi amfani da wannan Power ta sake shi to kar kuga laifin alƙalai babu ruwan su, laifin Gwamnati ne, ita kuma Gwamnati ba laifin ta bane laifin ƴan Majalisun ku ne saboda sune suka tsara dokar a haka.
Bissalam
Shehu Rahinat Na’Allah
3rd March, 2023