Hukumar zabe ta INEC ta yi alkawarin magance barazanar sayen kuri’u a zaɓen 2023.
Babban jami’in hukumar, Festus Okoye ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa kan zaɓen 2023 mai taken, “Me ke kawo kyakkyawan zabe a Najeriya,” inda ya ce hukumar za ta tura jami’an tsaro cikin sirri a ranar zaɓe.
Ya nanata kudurin hukumar na gudanar da sahihin zabe na gaskiya da adalci ga daukacin ‘yan Najeriya tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro.
Ya kara da cewa “za mu tabbatar da cewa babu wanda zai shiga wurin zaɓe da wayar salula da za ta iya daukar hoto”.
A cewar kwamishinan INEC, hukumar zabe za ta ci gaba da horar da ma’aikatanta wajen ganin an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali.