Sarki Charles III zai sayar da wasu daga cikin dawakan da ya gada daga mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth II.
Marigayiya Sarauniya ta kasance mai son dawaki kuma tana kiwonsu.
Gidan gwanjon kayayyaki na Tattersalls ya ce zai yi gwanjon dawaki 14 na Sarauniya a yau Litinin.
Daga cikin dawakin har da Just Fine wanda ya lashe tsere kusan 100.
Kakakin gidan gwanjon na Tattersalls ya ce ba wani sabon abu ba ne saboda a duk shekara suna sayar da dawaki.
Source:
Daily Nigeria
Via:
Zaharaddeen