A shirye-shirye domin tunkarar Zaben 2023 Kungiyar Yakin neman zaben Sanata Yakubu Lado Danmarke a matsayin Gwamnan jihar Katsina, ta Ladon Alkhairi Movement a aranar Lahadi biyu ga watan Oktoba, shugaban kungiyar ta Ladon Alkhairi Hon. Musa Yusuf Gafai, Sanata Yakubu Lado Danmarke, Hon. Salisu Yusuf Majigiri da sauran ‘Ya’yan kungiyar Ladon Alkhairi, da ‘Yan jam’iyyar PDP na jihar Katsina suka hallara a Hedkwatar Jam’iyyar PDP dake hanyar Kano, kusa da Ofishin jami’an tsaro na Civil Defance. Domin Ƙaddamar da wakilan kungiyar na dukkanin Rumfuna dake fadin jihar Katsina.

Kungiyar Ladon Alkhairi ta kasance kungiya mafi karfi da tsari daga cikin kungiyoyin yakin neman zaben Sanata Danmarke a matsayin Gwamnan Katsina, kamar yanda Shugaban jam’iyyar PDP ya bayyana a wani taron kaddamar da Motocin da kungiyar ta saya a kwanakin baya.
“Manufar kungiyar Ladon Alkhairi shine, kungiya ce da aka gina akan akida da tsari, wadda zata dunga gudanar da Ayyukan ta ko da Siyasa ko ba Siyasa, wannan kungiya zataci gaba da Jinkai da taimakon Al’umma a yanzu da lokacin zabe da bayan Anci zabe” Inji Sakataren Kungiyar, Hon. ‘Yantaba.

Hon. Musa Gafai ya bayyana Salo da Taken Kungiyar Ladon Alkhairi, kuma ya bayyana yanda zata gudanar da Ayyukan ta a lokacin zabe, sana an raba kayan Aiki irinsu Alluna masu Hoton Sanata Yakubu Lado Danmarke, da Ba-je, Uniform, Abayoyi Riguna da sauransu. A yayin da aka raba Allunan Kamfen ga ko wane Kansila a jihar Katsina a mazabar sa guda Ashirin kamar yanda Gafai ya bayyana, da kuma yanda za’ayi amfani dasu.
Hon. Majigiri ya bayyana kungiyar Ladon Alkhairi da cewa duk wani Dan jihar Katsina yasan da sunan wannan kungiya, yace sunje Ofishinta a jam’iyyance sunga irin Ayyukan ta, kungiya ce mai tsari, kuma ta tafi da Zababbun Kansilolinsu, na PDP da haryanzu yace a wajensu sune Kansiloli.

Hon. Majigiri a wajen taron ya tabo yanda zaben Kananan Hukumomi ya gudana dakuma irin tsarin da sukayi wanda har hukumar zabe ta tabbatar da ingancin tsarin. Ya kara da cewa duk da ka’ida tsarin da suke da shi, hakan bai hana jam’iyya mai mulki nada Kantomomi ba, yace don haka idan suka ci zabe kowa yasan Kwanannan zancen. A karshe yayi kira da su jajirce saboda yakin na Wajen su.

Dantakarar Gwamnan jihar Katsina Sanata Yakubu Lado Danmarke ya bayyana jin daÉ—in sa da samuwar Kungiyar Ladon Alkhairi inda yayi kira ga sauran kungiyoyi da suyi koyi da Kungiyar Ladon Alkhairi.
Yace “Idan da ana samun irin wadannan Kungiyoyi to babu wani Shakku, munsan cewa da Izinin Allah babu wani zabe da jam’iyyar PDP ba zata lasheshi ba.

Yace: lallai Kalu bale ne ga sauran kungiyoyi da su tashi tsaye suyi koyi, yace saboda ita kungiyar, kungiya ce da duk wani mai neman takara na jam’iyyar PDP take kokarin mara masa baya don ganin ya lashe zabe. Zamu kawo maku yanda taron ya gudana a bidiyo a shafukan mu na Katsina City News