Amadadin Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina KTSTA karkashin Jagorancin Alhaji Haruna Musa Rigoji.
Na sanar da Abokan Huddarta cewa hukumar sufuri ta Jiha ta janye sanarwar da ta bayar na tsaida amsar tsoffin kudi daga fasinjoji a Ranar 29/1/2023.
Don haka hukumar zata ci gaba da amsar tsoffin kudi daga hannun fasinjoji har zuwa ranar da Babban Banki Najeriya ya tsaida a Daina amsar tsoffin kudin.
Duk wanda yaga sanarwar da aka Bada can baya to kar ya damu da ita wannan itace aka tabbatattar magana. Da fatan Allah ya Kara bamu Zaman lafiya da Arziki Mai yalwa da inganci Amin.
Sanya hannu sakataren hukumar Alhaji Ibrahim Keegan Katsina.
Source:
Katsina City News
Via:
Katsina City News