Nan wasu likitoci ne a Lagos ke shirin yin jarrabawar komawa Birtaniya da aikiImage caption: Nan wasu likitoci ne a Lagos ke shirin yin jarrabawar komawa Birtaniya da aiki
Akalla likitoci ƴan Najeriya 162 ne aka bai wa takardar izinin aiki a Birtaniya a cikin mako shida da ya gabata, kamar yadda bayanan kundin hukumar da ke yi wa jami’an na lafiya rijista suka nuna.
Jaridar Punch ta Najeriya ta ruwaito cewa shafin intanet na hukuma rijistar (GMC) ya nuna cewa a cikin kwana 42 da suka wuce aka samu wannan ƙari, wanda hakan ya sa a yawan likitocin da suka koma Birtaniya da aiki daga Najeriya ya ƙaru daga 10,824 zuwa 10,986.
Ƙididdigar ta nuna a kowace rana ana yi wa aƙalla likita uku ƴan Najeriya rijista a Birtaniya, daga ranar 2 ga watan Fabarairu zuwa 15 ga watan Maris da muke ciki.
Najeriya ta jima tana fama da matsalar ƙaurar ƙwararrun ma’aikata da masana zuwa wasu ƙasashen duniya mafiya arziƙi domin samun albashi da kuma yanayin aiki mafi kyau.
Wasu bayanai na nuna cewa Najeriya ce ta uku a ƙasashen da suka fi yawan likitoci a Birtaniya, bayan India mai likitoci 31,979 da kuma Pakistan mai 18,490.
Nigeria has been faced with worrying brain drain in recent times, with many professionals, including doctors, leaving the country for greener pastures.