Daga Muhammad Kabir
Jaridar Taskar Labarai
Ɗan takarar gwamna a jam’iyyar NNPP Injiniya Nura Khalil ya fadi hakan ne a yayin da yake ganawa da dalibai da matasan jihar Katsina.
Wanda Youth Leader Nura Khalil Campaign Council Suka Shirya a ranar 19/2/2023 a dakin taro na Munaj Event Center dake a katsina.
Dan takarar yace ma aikaci zai yi shekara 35, ya kammala aikin gwamnati, duk karfinsa ya kare, amma bai da muhallin da zai zauna.
“Mu a gwamnatin Jam’iyyar NNPP idan allah ya kaimu ga nasara zamuyi tsari da kuwane ma’aikaci zai mallaki gidan kansa.
Khalil ya kara da cewa, babana ma’aikacin Gwamnati ne amma har ya bar duniya bai mallaki gidan kanshi ba sai na ga do, don haka na sha alwashin in Katsinawa suka bani dama sai kowane ma’aikaci a katsina ya mallaki gidan kansa kafin ya yi ritaya daga aiki.
A bangaren Ilimi kuma dan takarar yace “An wayi gari dalibai basa iya zama zana jarabawar neco ko waec. Saboda bakin ciki da keta ta Shuwagabanni.”
“Kuma bayan a lokacin da su sukai karatun an basu kumai kyauta. kamada kayan makaranta, sabulu, maganin sauro, dadai sauran su.”
“A yanzu an wayi gari idan mahaifinka baida dubu ashirin da zai biya maka jarabawa, daganan karatun ya tsaya.”
Engr Nura Khalil yacigaba da cewa, sai a ɗauki kudin gwamnati a ba ashararar, ko a kirkiro wasu kwangiloli na bugi. Amma gwamnati ba ta damu da rayuwar matasaba.
Injiniya Nura Khalil yace Idan Allah ya kaisu ga nasara Zasu ba fannin Ilimi Muhimmancin.
Daga karshe yayi kira ga daliban da suka halacci taron dasu fito a ranar zaɓe, suyi anfani da katin su su fillema azzalumai kawuna. Kuma su tabbatar sun zaɓi jam’iyyar NNPP daga sama har Ƙasa