Muazu Hassan Katsina City News
Mataimakin shugaban jam iyyar PDP na katsina, Alhaji Salisu Lawal Uli ya shigar da kara a gaban babbar kotun tarayya ta katsina akan shugabancin jam iyyar PDP a jahar katsina.
Alhaji salisu Uli ya na neman kotu ta bayyana wane halastaccen shugaban jam iyyar PDP a katsina tsakanin Alhaji salisu Yusufu majigiri da lawal Magaji Dan baci.
A zaman kotun na yau an saurari karar, an kuma daga zuwa 29 ga watan Nawumba don cigaba da Shari ar.
Shari ar mai taken tsakanin, salisu Uli, hukumar zabe ta kasa da kuma sabon shugaban da nada Alhaji lawal Magaji Dan baci.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
[email protected]