@ katsina city news
Dalilin Dagawar shine lauyan Masu kara, shine ya aiko ma da kotu takardar baya da lafiya, a canza masa zuwa wata Rana.
Alkalin kotun tarayya dake katsina, ya amshi uzurin lauyan ya kuma daga Shari ar zuwa 15 ga watan Disamba.
Shari ar dai Alhaji salisu lawal Uli ya shigar da ita,akan sabon shugaban jam iyyar PDP na jahar katsina da uwar jam iyya ta kasa ta nada.
Uli, Yana bukatar kotun ta ayyana wanene shugaban jam iyyar PDP na gaskiya bisa tsarin mulkin PDP. Tsakanin sabon shugaban da kuma Alhaji salisu Yusufu majigiri.
Uli, yana kuma bukatar kotun ta bada umurnin, PDP ta koma yadda take a tsarin shugabanci har sai an kammala Shari ar
@ katsina city news
Www.katsinacitynews.com