Zaharaddeen Mziag @Katsina City News 11/112022
“Rayuwata na cikin Hatsari, saboda daƙile satar ɗanyen Mai” -Mele Kyari
Shugaban Kamfanin NNPC Malam Mele Kyari ya bayyana cewa rayuwasa tana cikin Hatsari sakamakon barazana da ake yi masa don ƙoƙarin Gwamnatin tarayya na daƙile hana satar gurɓataccen Mai. Keri da yake jawabi a wajen wani taro akan muhimmancin gudanar da shugabanci a Faifai wanda kwamitin yaki da rashawa na majalisar wakilai ta tarayya ta shirya a Abuja. Ya bayyana damuwarsa a kan yanda Najeriya ke asarar Gangar Danyen mai dubu ɗari bakwai a ko wace rana sakamakon ɓarayi dake sace ɗanyen main kamar yanda ya bayyana cewa a karan farko tun bayan shigarsa ofishinsa daga watan Yuli na wannan shekara gwamnatin ƙasar ta fara haƙo kimanin gangar mai miliyan ɗaya a kowace rana, inda daga watan Oktoba da ya gabata kuma adadin ɗayanyen mai da ake samu ya ƙaru zuwa ganga miliyan ɗaya da dubu sha hudu 14.