Kungiyar yarabawa ta Oodua People’s Congress (OPC) ta buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya saurari kiran da gwamnonin jihohi su ka yi na ya ba su damar samun ingantattun kayan aiki don dakile ayyukan ƴan bindiga da ƴan ta’adda a jihohinsu.
Kungiyar ta kuma buƙaci shugaban kasar da ya sake duba, tare da aiwatar da kudurorin taron kasa na shekarar 2014, kafin mika mulki a shekarar 2023.
Jaridar Punch ta rawaito cewa, a cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren kungiyar, Bunmi Fasehun, a madadin shugaban ƙungiyar, Otunba Wasiu Afolabi ne ya bayar da shawarar a Legas a ranar Litinin.
Afolabi ya jaddada cewa, “Ta hanyar hana gwamnoni wadannan makamai, ya nuna cewa fadar shugaban kasa na goyon bayan ‘yan ta’adda a kan ‘yan Najeriya masu bin doka da oda, wadanda ake garkuwa da su, fyade, yankan rago da gudun hijira zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira. Lokaci ya yi da ya kamata gwamnatin tarayya ta bi sahun jama’a a fili wajen yakar wadannan namun daji na wata kasa (kamar yadda Fela Anikulapo-Kuti ya kira su) da ke barazana ga rayuks da dukiyoyi.
“Babban burin gwamnati shi ne samar da tsaro ga jama’a. Duk gwamnatin da ta gaza a kan wannan nauyi na farko na samar da tsaro, to ta gaza.” Ya kara da cewa.
Sai dai ya taya shugaban kasar murnar sako sauran wadanda aka yi garkuwa da su a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.