Daga Badaradeen Muhammad Abuja
Bayan sun jikkata jama’ah, Jami’an VIO sun jikkata kansu a wani hatsarin mota da suka yi a Abuja yayin da suke fafarar wani direban da suke zargin takardunsa sun kare kuma bai sabunta ba.
Hatsarin wanda ya afku da misalin karfe 3:10 na yammacin ranar Litinin, 19 ga watan Satumba, jami’an VIO ne da ke tuki a kan “Hanya Daya” a yayin da suke bin wata mota a gadar Lugbe da ke kan titin filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe a Abuja.
An tattaro cewa jami’an na tukin mota ne a kan gadar a kokarin da suke na cafke wani direban da ake zargin takardar motarsa ta kare amma ana cikin haka ne suka yi karo da wata mota kirar Toyota Corolla da ke tahowa mai lamba ABJ 717. CE.
An garzaya da jami’an na VIO da suka jikkata zuwa asibiti. Motocin biyu da abin ya shafa sun lalace matuka.
Lamarin da ya janyo hankulan dimbin masu wucewa da kuma jama’a da suka yi tururuwa zuwa wurin, inda suka zargi jami’an na VIO da haddasa hatsarin.
Direban motar (Ibrahim) wanda ya tsallake rijiya da baya a lokacin da yake bada labarin abin da ya faru da shi, ya ce yana hawan gadar ne kwatsam ya ga motar VIO ta taho daga wani bangare a guje inda idonsu ya rufe suka kasa kallon kowa in banda abin farautarsa.
Ibrahim ya ce Allah ne ya tseratar da rayuwarsa da yanzu anyi jana’izarsa.
Ko kunga da cewar bin jama’ah a guje haka?