Daga Danjuma Katsina
A rana mai kamar ta yau ce, na jagoranci wasu dalibai Musulmi muka tarwatsa gungun wasu dalibai da ke bukin ranar Valentine a Sculpture Garden da ke ABU Zariya.
Wannan lamarin ya faru ne a daren 14 ga watan Fabrairu, 1991.
Mu shida muka kitsa farmakin. Ni, Danjuma; wanda na tsara na kuma shugabanta, sai Ibrahim Potiskum, Abdulmumini Giwa; yanzu shi ne Editan Jiha na jaridun VANGUARD a Kano, Dakta Samir Yusuf; yanzu yana koyarwa a ABU Zaria, Muhammad Balkore; yanzu yana Abuja, Alhaji Mamu; yana Abuja, bayan ya gama karatun Likita a kasar Iran, sai wadanda suka rufa mana baya.
Mun tsara komai ne a babban masallacin Juma’a na ABU, amma daga dakin su Malam Ibrahim Potiskum da ke Magume 4, Room 5.
Bayan kai farmakin kungiyar dalibai Musulmi ta Jami’ar sun yi Allah wadai da aikinmu, suka nemi Hukumar makaranta ta dau mataki a kanmu.
A lokacin ina cikin zababbu shugabannin kungiyar dalibai Musulmi na Jami’ar a matsayin Editan Mujallar Kungiyar da ake kira THE WISDOM.
A ranar 16 ga Fabrairu, 1991 kwana biyu bayan farmakin ranar Valentine na kira taro a babban masallacin Juma’ar Jami’ar, inda na shelanta rusa shugabancin kungiyar dalibai Musulmi na Jami’ar da kafa wani kwamiti da zai rika sa ido a kan harkokin dalibai Musulmi na jami’ar kafin a gudanar da sabon zabe. Sunan kwamitin, Shura Committee.
Kwamitin Shura shi ne ya jagoranci bukin kona Mujallun LOLLY da FUNTIMES a Jami’ar ta ABU, saboda wani rubutu da zane na cin zarafin Manzon Allah (SAW).
Rikicin ya yadu kusan duk manyan makarantun kasar nan, wanda ya haifar da wata shela a Katsina, inda Gwamnan soja na lokacin ya ce zai sanya a kama Malam Yakubu Yahaya ya kai shi filin Polo ya harbe shi.
Rayuwa ke nan. Allah ya kara mana kwanaki masu albarka da taimakon Musulunci da al’umma baki daya.
Danjuma Katsina 14/2/2023