Mahmood Hassan @Katsina City News
Hedkwatar jam iyyar PDP ta kasa,ta aika da wasiku ga shugabanin PDP na jihohin kasar nan, akan yunkurin da akeyi na tsige shugabanni a wasu jihohi.
Wasikar wadda jaridun katsina city news suka ga kwafi an rubuta ta a ranar 1/11/2022. Wanda ya Sanya mata hannu shine sakataren tsare tsare na jam iyyar, Hon Umar M Bature.
Takardar na cewa, kwamitin gudanarwar jam iyyar PDP na kasa,ya lura, wasu da basu bukatar zaman lafiya a jam iyyar na kokarin kawo rudu a cikin jam iyyar da yunkurin tsige ciyamomin jihohin su.
Takardar ta ci gaba da cewa, yana da kyau kowa ya sani cewa,PDP jam iyya ce, wadda doka da tsarin mulki shine ke tafiyar da ita.
Kuma duk tsige ko ladabtar da wani a cikin jam iyyar dole A bi ka ida da doka, kamar yadda tsarin mulkin jam iyyar na sekshen na 57(7) yace.
Takardar taci gaba da cewa, yana da kyau duk wani, Dan jam iyya ya sani, sabama tsarin mulkin jam iyya ne na sekshen 58(1)(a)(b)(c)(i)da kuma(j). kin bin umurnin da kwamitin gudanarwar jam iyyar ya bayar.kuma Wanda yaki bin wannan umurnin, za a iya ladabtar dashi a karkashin sekshen na 59(1) na tsarin mulkin jam iyyar PDP wanda aka gyara a shekarar 2017.
Kamar yadda aka sani jahar katsina na cikin inda wannan badakala take faruwa.kuma tana cikin inda Wannan takarda ta shafa.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
[email protected]