PDP ta ce za ta garzaya kotu don amfanin mutanen Katsina.
Majalisar yakin neman zaben jam’iyyar Peoples Democratic Party a jihar Katsina ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar.
Hakan na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana Dr. Dikko Umaru Radda a matsayin zababben gwamna a karshen tattara sakamakon zaben a ranar Litinin.
Jam’iyyar adawar ta yi zargin cewa gwamnatin da ke mulki ta umarci dukkan shugabannin kananan hukumomin da su tabbatar sun kada kuri’ar APC tun daga sama har kasa ta kowane hali.
Darakta Janar na kungiyar yakin neman zaben Atiku/Lado, Dokta Mustapha Inuwa, a wata ganawa da manema labarai a ranar Litinin, ya yi imanin cewa zaben ya kasance da kura-kurai da dama kamar tursasawa da cin zarafin wadanda suka cancanci kada kuri’a da dai sauransu.
Inuwa yayin da ya yi barazanar zuwa kotu domin kalubalantar yadda aka gudanar da zaben da kuma sakamakon zaben, ya bayyana cewa kuri’un da aka ce an kada a zaben sun zarce na zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya duk da karancin fitowar masu kada kuri’a a jihar.
“Ba mu damu da faduwa zabe ba amma kokarin da jam’iyyar All Progressives Congress ke yi na dakile dimokuradiyya. Zamu garzaya kotu don amfanin al’ummar Katsina.
“A inda jam’iyyun APC da PDP suka samu kuri’u kasa da miliyan daya a zabukan da suka gabata, PDP ce ke da mafi girma. Amma yanzu duk da karancin fitowar jama’a da mutane da yawa ke ganin cewa kasa da kashi 50 cikin 100 na wadanda suka fito zaben da ya gabata ba za su iya fitowa a wannan karon ba amma rabon kuri’u ya koma APC ya ninka na baya,” ya bayyana. .