• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Friday, March 31, 2023
  • Login
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Sashen Hausa

PDP da Atiku sun janye ƙarar duba kayan zaɓe

March 15, 2023
in Sashen Hausa
0
Muna so a dakatar da sanar da sakamakon zaɓe – Kwamitin yakin zaɓen Atiku
0
SHARES
70
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP, wato Atiku Abubakar, shi da jam’iyyarsa sun janye sabuwar ƙarar da suka shigar ta neman tilasta wa hukumar zaɓe ba su damar duba kayan da aka yi amfani da su a zaɓen ranar 25 ga watan Fabarairu.

Atikun da jam’iyyarsa da ke ƙalubalantar sakamakon zaɓen da aka ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam’iyya mai mulki APC a matsayin wanda ya ci zaɓen, sun sheda wa kotun musamman da ke sauarren ƙararraki kan zaɓen shugaban ƙasar a Abuja cewa ba su da buƙatar ci gaba da ƙarar.

Jagoran ayarin lauyoyin da ke wakiltar Atikun da PDP Mista Joe-Kyari Gadzama (SAN) shi ne ya sheda wa kotun haka lokacin da aka zauna fara sauraren ƙarar a yau Laraba.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa wani daga cikin lauyoyin na Atiku da PDP, wanda bai yarda a ambaci sunansa ba, ya ce tun da farko sun shigar da ƙarar ne saboda matsaloli da ƙalubalen da suka gamu da su lokacin da wakilan jam’iyyar da Atiku suka je hukumar zaɓen domin a ba su kayan su duba, kamar yadda kotu ta bayar da umarni.

Ya ce, to kasancewar kafin a zo sauraren wannan ƙara da suka shigar ta tilasta wa INEC barin wakilan su duba kayan zaɓen, INEC da kanta ta fito ta yi alƙawarin ba su damar su je su duba wasu daga cikin kayan musamman ma takardar da aka yi zaɓe, ya ce saboda haka ne suka janye wannan sabuwar ƙara.

Atiku da jam’iyyar tasa da kuma ɗan takarar Labour shi ma da jam’iyyar tasa dukkaninsu suna ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasar na Najeriya, inda kowanne daga cikin ɓangaororin biyu ke iƙirarin shi ne ya yi nasara aka yi masa fashi, tare da lasar takobin ƙwato nasarar tasu.

Share

Related

Source: BBC Hausa
Via: Katsina City News
Previous Post

Girmanka Akwatinka: “Wallahi-Wallahi tallan da Rarara Yakeyi na Gawuna Akwai mugunta” -Nabraska

Next Post

Brief History Of Sardaunan Katsina,Amb. Ahmed Rufai Abubakar, CFR

Next Post
Brief History Of Sardaunan Katsina,Amb. Ahmed Rufai Abubakar, CFR

Brief History Of Sardaunan Katsina,Amb. Ahmed Rufai Abubakar, CFR

Recent Posts

  • On birthday, clerics pray for Tinubu, Nigeria in Abuja
  • Gwamna Masari ya Kaddamar da Kwamitin Miƙa Mulki ga sabuwar Gwamnati
  • Masari: Tinubu Na Bukatar Addu’a
  • Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Karu Zuwa N46.25tr —DMO
  • FEC Approves N59.78bn For Ogoni Cleanup Projects

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • March 2023
  • February 2023
  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In