Daga Zaharaddeen Gandu
Lado Ɗanmarke yace, Allah ya albarkaci jam’iyyar PDP da ‘yan kasuwa bila’adadin kuma duk dankasuwa yasan yadda zai maida 5 ta koma 10.
Yace, duk wanda baisa yadda zai maida 5 ta koma goma ba irin su ne ke wulakanta dukiyar talakawa a wofi musamman a mulkin jam’iyyar APC.
Ya bayyana hakan ne a dakin taro na Event Centre a lokacin da ya jagoranci kaddamar da kungiyar ‘yan kasuwa reshen jihar Katsina.
Ya bada tabbacin cewa, kamar yadda ɗantakarar Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar dankasuwa, ɗantakarar gwamnan jihar Katsina dankasuwa, da duk ‘yan takarar Sanatoci 3 na Katsina duk ‘yan kasuwa, haka ‘yan takarar majalisar jihar Katsina a jam’iyyar PDP ‘yan kasuwa, yace ‘yan takarar jam’iyyar PDP kashi 80 cikin 100 a jihar Katsina duk ‘yan kasuwa ne.
Ɗantakarar gwamnan ya kara da cewa, da yawan ‘yan jam’iyyar APC basu san yadda ake kasuwanci ba shiyasa kullum komai ke kara tabarbarewa a najeriya, yace sun hau mulki basusan yadda ake tara kudi ba saide kawai su kashe.
Ya jaddada cewa, duk inda dankasuwa yake yasan darajar kudi kuma yana da su ba zai hangi na wasu ba har yayi burin barnatar da su a wofi, yace za su yi iya kokarinsu su rike amanar dukiyar talakawa a kan yadda ya dace idan suka ci zaben shekarar 2023.
Ya kara jaddada cewa, ya kamata al’umma su hankalta a kan cin amanar da jamiyyar APC ta yi musu ta bangarori da dama a fadin Najeriya da jihar Katsina baki daya, yace an hana talaka Noma, an hana su yin kasuwanci da karfin tsiya an kakaba ma talakawa fatara da yunwa.