…An yi zaben dan takarar Majalisar Tarayya na Malumfashi
Muazu Hassan &
Zaharaddeen Ishaq
@Katsina City News
Jam’iyyar PDP ta Jihar Katsina ta yi watsi da hukuncin kotun Tarayya da ke Katsina a karar da Murtala Shehu ya shigar a kanta da kuma abokin takararsa, Nasiru Saad Ahmad da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC). tayi gaban kanta ta gudanar da zaben fitar da Dan malumfashi da kafur.
Murtala Shehu, wanda ya tsaya takarar dan Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kafur da Malumfashi, ya shigar da kara a babbar kotun Tarayya da ke Katsina yana kalubalantar zaben fitar da dan takarar da jam’iyyar PDP ta gudanar, wanda zaben ya bai wa Nasiru Saad Ahmad nasara.

A hukuncin da Alkalin kotun, Alhaji Muhammad Shitu Abubakar ya karanta ranar 24 ga watan Nawumba, 2022, ya soke zaben da cewa bai inganta ba. Sannan ya nemi a sake sabon zabe cikin makonni biyu. Ya kuma ba da damar wanda ya shigar da karar yana iya daukaka kara a kotu ta gaba idan bai gamsu ba.
A ranar 25 ga watan Nuwamba, wanda ke karar Murtala Shehu ya ba da shelar tabbatar da daukaka kara zuwa kotu ta gaba.
Lauyansa ya sanar da kotun Tarayya ta Katsina, ya kuma sanar da hedikwatar PDP ta Jiha, cewa ya dauka ka karar.
Kuma a ranar ta 25 ga wata mai bai wa jam’iyyar PDP ta Jiha Katsina shawara a kan harkokin shari’a, MS Mahuta MNIM, ya rubuta wa hedikwatar PDP ta kasa cewa, shari’ar da ake yi a kan zaben fitar da dan takarar Majalisar Tarayya na Kafur da Malumfashi, wanda ya shigar da karar ya daukaka kara zuwa kotun daukaka kara.
Hedikwatar PDP ta tabbatar da amsar wasikar har ta sanya mata hannu da buga kan Sarki.

Duk da wannan daukaka kara da Murtala Shehu ya yi, a ranar Asabar 10/12/2022 jam’iyyar PDP ta yi gaban kanta ta gudanar da zaben fitar dan takara a mazabar.
PDP ta yi zaben kwanaki 16 da yanke hukuncin, bayan kuma Alkalin kotun cewa ya yi a canza zaben kwanaki 14 da yanke hukuncin.
Wakilanmu sun halarci zaben da aka yi a garin na Malumfashi, wanda dan takara daya tilo wato Aminu Sa’ad ya shiga.kuma aka shelanta shine ya zabe.
Wakilanmu ya lura an fara zaben a kurarren lokaci, aka gama cikin gaggawa, duk da sarakakkiyar da zaben ke da shi na shari’a, an daukaka kara a kan hukuncin, an kuma kara kwanaki daga yadda Alkalin ya ba da umurni a hukuncinsa.
Jam’iyyar PDP dai ta dare gida biyu a Jihar Katsina, yayin da bangare daya na kotu, bangare daya kuma ya samu goyon bayan hedikwatar jam’iyya ta kasa, wadanda ake kira bangaren Ibrahim Shema, tsohon Gwamnan Katsina da kuma bangaren Sanata Yakubu Lado Dan Marke dan takarar Gwamna a jam’iyyar PDP.
Bangaren da suka yi fatali da hukuncin na kotu shi ne Sanata Yakubu Lado Dan Marke, yayin da Murtala Shehu yake dan bangaren Ibrahim Shema.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
Email [email protected]