Muhammad A. Ali @Katsina City News

Ofishin Babban Darakta na Yaƙin neman Zaben Dantakarar Shugaban ƙasa da Gwamna a jam’iyyar PDP, Dakta Mustapha Muhammad Inuwa shine Ofishi mafi girma da ƙarfi, idan aka cire Babbar Hedkwatar Jam’iyyar PDP a Katsina.
Shine Ofis mafi girman Daraja da Ƙarfi a Siyasar Katsina, wanda Asalin Ofishin na yaƙin Neman Zaben Dakta Mustapha Inuwa ne, tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Katsina a lokcin yana Neman takarar Gwamna a jam’iyyar APC kafin zaben fitar da Gwani wanda yabawa Dakta Dikko Umar Radda Nasara a lokacin da shi kuma Dantakarar Mustapha Inuwa yazo na biyu.
A lokaci guda bayan abinda ya faru ya faru, jam’iyyu daban-daban sukayi ta Zawarcin tsohon Sakataren Gwamnatin Dakta Inuwa domin ya mara masu baya ganin irin karfi da tasirinsa a Siyasar jihar Katsina, a karshe dai Babbar jam’iyyar Adawa ta PDP ce tayi Nasarar Zabaro Dakaren Siyasar inda yayi Wuf da ita, cikakken Aure mai igiya uku. Wanda hakan yasa Ofishin ya kara ƙarfi, da ƙarfin faɗa a Ji a jam’iyyar PDP, takai duk abinda ya fita indai ba daga Ofis din bane, kamar shafa labari shuni ne. Duk wani zama duk wani Mitin na Siyasa Safe ko Dare, zuwa karɓar ƙungiyoyi a Ofishin ake yinsa, “amma kafin bayyanar Ofishin akwai ofisoshi da suke matukar kaɗa bazar Siyasa” Duk wani ƙusa a jam’iyyar PDP babu wanda baije ofishin akayi mitin da shi ba idan ka cire tsohon Gwamnan jihar Katsina, Barasta Ibrahim Shehu Shema, wanda yake ganin kamar wannan Aure da aka ɗaura da tsohon Sakataren Gwamnati Mustapha Inuwa da jam’iyyar PDP bai Ɗauru ba. “A gefe guda kuma wasu na kallon kamar Aure cikin Aure akayi, kuma abinda ka iya biyo bayan wannan shine Saki.”
Ko ba a bayyana ba bayan Zaben Shugaban ƙasa, ‘Ya’yan jam’iyyar PDP da dama zuciyarsu tayi sanyi sun karaya musamman a jihar ta Katsina, saɓanin wasu jihohi inda a lokacin ne suka ɗaura Ɗamarar ganin bayan jam’iyya mai mulki a jihohinsu, irinsu Kano da Zamfara.
Daga Zaben Shugaban ƙasa bayan makwanni biyu aka gudanar da zaben Gwamna inda jam’iyyar PDP ta sha ƙasa da gagarumin rinjaye inda jam’iyyar APC tayi Nasara.
Ƙasa ga wata guda da gudanar da zaɓen sai ya zamana Babban Ofishin yayi wata ‘yar gajeruwar suma, inda yazama Tsit, hatta Matasan da ke yayyafawa Ofishin ruwa don ya Farfaɗo suma sun sare don sunga alama kamar doguwar suma ce yayi.
Katsina City News ta hango ofishin an Ciccire duk wata Fasta, ko Sitika da Bana mai Alamar Dantakara ko jam’iyyar PDP, hakan ya sanya Alamar kowa ke tambaya shin Ofishin mai karfi kamar Zaki, ya Mutu kenan ko kuwa?
Koda yake kafin Doguwar Sumar da Ofishin yayi, Daraktan yakin neman Zabe na PDP dashi da Dantakarar Gwamnan Senata Yakubu Lado da sauran Muƙarraban PDP sun kira wani taron manema labarai inda suka bayyana yanda zaben ya gudana kuma sukace zasu dauki mataki na Shari’a. Amma daga bisani jaridun Katsina City News sun jiwo wata majiya mai karfi tana cewa PDP ba zataje Kotu ba, sun barwa Allah. Harma mataimakin shugaban Jam’iyyar APC na jihar Katsina Bala Abu Musawa yayi tsokaci akan batun. Inda ya bayyana cewa su suna ja akan wasu kujeri nasu da suke ganin PDP tayi magudi a yankunan.
A gefe guda kuma wasu na ganin daɗin ne yayiwa APC yawa.
Koma dai minene, anyi zaɓe saura rantsar da sabuwar Gwamnati da ganin ita kuma dami tazo dashi. Sana kuma mutanen Katsina sun zura Ido suga ina Makomar PDP da Uwar Jam’iyya ta Ƙasa ta rosa shugabanninta kuma ta kafa na ruƙwan ƙwarya kwana Casa’in domin Gyaran fasalin jam’iyyar.