Jam’iyyar adawa ta NNPP da kungiyoyin farar hula, ƙarƙashin inuwar ‘Alliance for Good Governance’ sun bukaci da a gaggauta gurfanar da wani shugaba a jam’iyyar APC, Aliyu Shana da aka kama da katin zaɓe na dindindin guda 300 a Kano.
Shana, wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC na unguwar Yautan Arewa, Ƙaramar Hukumar Gabasawa a jihar Kano, ya shiga hannun ƴan sanda a jiya Juma’a, tare da mika shi zuwa shelkwatar rundunar domin bincikar sa.
DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa mallakar katin zabe ba bisa ka’ida kuma na ɗauke da sunan wasu ya saɓa wa sashe na 21 da 22 karamin sashe na 1 (a), (b) da (c) na dokar zaɓe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima.
A wata sanarwa da shugaban NNPP na jihar, Umar Doguwa ya fitar, ya ce jam’iyyar ta umurci lauyoyin ta da su shigar da kara a kan wanda ake zargin da kuma waɗanda su ka sa shi ya aikata.
“Na umarci mai ba mu shawara kan harkokin shari’a da ya rubuta wa alkalan zabe (INEC) don bibiyar matakin da ya dace a kan lamarin,” in ji Doguwa.
Ya ce batun ɓoye katin zabe na PVC ya zama babban abin damuwa a Kano gabanin zaben 2023.
“Wannan kamen ya tabbatar da gaskiyarmu mu, za kuma mu tsaya tsayin-daka mu ga matakai na gaba da hukumar zabe mai zaman kanta da ƴan sandan Nijeriya za su dauka,” inji shi.
Jam’iyyar NNPP ta ce za ta ci gaba da bin shari’ar har zuwa tiƙewa domin kare martabar dimokuradiyya.
Shugaban jam’iyyar ya yaba da kokarin da rundunar ƴan sandan jihar Kano ke yi na tabbatar da gudanar da bincike mai inganci kan lamarin.