Gwamnatin Nijeriya ta fitar da wasu shawarwari ga ƴan ƙasarta masu zuwa ƙasashen Amurka da na Tarayyar Burtaniya da sauran ƙasashen Turai.
A wani taron manema labaru da ya gudana yau Litinin a Abuja, ministan yaɗa labaru na Najeriya Lai Mohammed ya ce an fitar da shawarwarin ne bayan rahotanni na kai wa ƴan Najeriya hari da ƙwace masu kaya a ƙasashen waje, ciki har da birnin London.
Mohammed ya ce ana karɓe wa mutanen da suka fito daga Najeriya kaya, ciki har da kuɗi da fasfo na tafiye-tafiye.
Saboda haka ya ce ya kamata ƴan Najeriya da ke tafiye-tafiye zuwa ƙasashen nahiyar Turai da Amurka su rinƙa yin taka-tsantsan.
Hakan zai iya zama kamar ramuwar gayya ga ƙasashen turai bayan da a kwanakin baya ƙasashen Amurka da Birtaniya da kuma wasu daban suka gargaɗi al’ummarsu daga zuwa Najeriya saboda rashin tsaro da ake fama da shi.