Ɗantakarar Mataimakin Shugaban Kasa na jam’iyyar Labour Party L.P dake Marawa Peter Obi baya Dakta Yusuf Datti Baba Ahamed ne ya bayyana haka a ranar Lahadi Lokacin da yake ganawa da Jaridar Katsina City News a masaukinsa bayan taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ta Labour Party da ya gudana.
Datti Ahamed ya ce Shi dangidan Malamai ne yana matukar kwadayin ayi Siyasar Addini Amma idan za’ayi dagaske amma a fito da Shehinnai da Manyan Malamai dayansu ya zama shugaban kasa dayansu ya zama mataimaki. Ya kasance Gwamnoni da Sanatoci duk malamai ne, ba wai Dansiyasa da zai fito takara akansa ko Sabbi babu. Yace ‘Yan siyasa sunbar Malamai a Zaure suna yaudarar su suna Cutar su, da sunan Siyasar Addini. Yace “Dimokuraɗiyyar abinda ya shafi rayuwar Bil’adama ne, Addinin mu daban babu abinda ke tabashi ba kuma zamu bari a gurbatamana Addini da Shiriritar Siyasa ba, kada mu sake bari a yi Siyasar Addini, saboda anyi na Addini al’ummar musulmi suka wulakanta, duk Duniya babu inda mutane suka wulakanta kamar Arewacin Najeriya a yanzu kuma aje a duba. Matan da akewa wulakanci, yaran da ake hanawa karatu, mutanen da aka hana Noma, aka kora wasu aka kashe, a taron mu ma saida mukayi masu Addu’a ta musamman” inda Datti. A karshe yayi kira da itama siyasar Kabilanci a kaucemata, yace a kasarnan mutum uku ne ake tunanin zasuyi Shugaban kasa, don haka a duba Cancanta, a kalli Dattakon Peter Obi, da nazari akan dukkanin su a tace, Obi duk yafisu Cancanta.