Hukumar kula da kafafen yada labarai ta Najeriya NBC gargadi kafafen na yada labarai akan su kaucewa kayada karya da batanci domin tabbatar da ganin an gudanar da zubuka masu zuwa cikin kwanciyar hankali da lumana.
Shugaban hukumar Alhaji Shehu Illela shine ya bayyana haka a wajen taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya a Kano.
Illela yace dalilin shirya taron don a tattauna da shugabannin kafafen yada labarai na Rediyo da Talabijin, jami’an hukumar Zabe da sauran masu ruwa da tsaki don samun nasarar gudanar da zabubbuka Masu zuwa, bisa haka ne Alhaji Shehu Illela ya bukaci gidajen rediyo da talabijin da kada su bari ayi amfani dasu wajen yada kalaman karya da batanci don kaucewa afkuwar rikice-rikice yayin gudanar da zabuka masu zuwa.
Yace “Za’afara yakin neman Zabe Kwanannan, kafafen yada labarai sunada muhimmiyar rawa da zasu taka idan muka bar kafafen yada labarai sukayi abinda sukaga dama to za aiya wargaza kasar gabaki daya donnhaka dole ne muka kirasu a matsayinmu na masu sa ido a tsakanin s, mu gwadamasu cewa bafa zamu bari wata kafar watsa labarai ta bari ayi mafani da ita don cin mutumci wani ko cinzarafin wani ba.”
Yace duk gidan rediyo ko na talabijin da ya karya doka to doka zatai aiki akansa.
Da yake jawabi yayin bude taron Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa hukumar ta NBC wajen shirya wannan taron tattaunawar musamman a wannan lokaci da ake shirin fara yakin neman Zabe.
Taron ya samu halartar shugabannin gidajen rediyo da talabijin na yankin Arewa maso yammaci da Arewa maso gabashin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki na kafafen watsa labarai.