A Najeriya hukumar tsaron cikin gida ta DSS ta ce akwai wasu bata gari da suke kitsa tashin hankali don ganin fada ya barke a fadin kasar
Wannan na zuwa ne makwanni 2 bayan da hukumar ta yi irin wannan kashedi, inda ta ke shawartar ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki su bi hanyar doka wajen neman hakkokinsu a kan abin da ya shafi zabe.
A wata sanarwar da hukumar DSS din ta fitar, kakinta, Peter Afunanya ya ce a yayin da wasu ‘yan siyasa suka kai korafe-korafensu kotu, wasu na furta kalaman da ka iya kawo tashin hankali.
Afunanya ya gargadi masu yada labaran karya da zummar gwara kan al’umma da gwamnati mai ci, da su daina tun kafin rana ta baci musu.