Mutanen Unguwar Chake a garin Katsina sun Koka da rashin kwashe masu Shara daga hukumar SEPA.
Daga KATSINA CITY NEWS
Gidan Shara dake Unguwar Chake (Filin Bugu) a garin Katsina ya cika ya batse da Shara har ya Daidaita da saman rufin makwabta, inda Al’umar unguwar suka ce suna cikin fargaba duba da akwai wata Kwalbati da mafi yawa daga ruwan Unguwar tanan yake fita ga shi, kuma ana malkar damuna ruwa ba kakkautawa.
Sunce a koda yaushe fargabarsu kada Kwalbatin ta ida cikewa ruwa yayi ambaliya a cikin Unguwar, sunce hukumar SEPA a baya ta saba ta turo ma’aikatan ta su kwashe Saharar kafinta taru, amma daga bisani aka daina kwashewa, har ta kaiga tayi yawan da ya zama barazana ga Lafiya da Dukiyar al’umar yankin.
Sunce sunkai koken su ga hukumar SEPA; da suka zo da motar kwashe Shara sai gas ya Æ™are, tunda aka ganganÉ—a aka zuba masu Lita goma na gas, suka kama gabansu basu Æ™ara komawa ba. ‘Yan Unguwar ta Chake sunce; sunyi kwamiti sunje wajen SEPA da nufin sake dawowa a kwashe sharar sai Mutanen SEPA suka ce sai sun biya dubu É—ari uku kuÉ—in Gas sana a kwashe masu sharar.
Gidan sharar yana makwabtaka da tsohon gidan Sakataren Gwamnati jihar Katsina Alh. Muntari Lawal.

A farko-farkon Mulkin Gwamnatin Katsina ƙarƙashin Jagorancin Rt. Hon. Aminu Bello Masari yayi kokarin kafa wani kwamiti da ke kula da tsaftace gari, inda aka sanyawa Kwamitin Tsafta Cikon Addini, wanda aka dunga bi lungu da saƙo na cikin Birnin Katsina ana kwashe duk wani datti ko shara da take cikin Lunguna inda da dama daga matasa suka samu Aikin yi. A wani jawabi da mai girma Gwamnan Katsina Aminu Masari ya taɓa yi wajen Kaddamar da Kwamitin na Tsafta cikon Addini a Unguwar Filin Folo, yace yana so ya maida Katsina kamar Kalaba a ɓangaren tsafta.
A karshe dai Al’umar Unguwar suna roÆ™on Gwamnati ta duba yiyuwar kwashe Saharar cikin sauri kada Æ™aramar Matsala ta zama babba.