Honarabul Musa Gafai Ya Zama Daraktan Tuntuɓa Da Tattara Al’umma Na Tawagar Yaƙin Neman Zaɓen Atiku Da Lado Danmarke A Jihar Katsina

Uwar Jam’iyyar PDP Ta Kasa Ta Naɗa Hazikin Matashin Ɗan Siyasar Nan Kuma Shahararren Ɗan Kasuwar Nan Na Jihar Katsina, Honarabul Musa Yusuf Gafai Daraktan Tuntuɓa Da Tattara Al’umma Na Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa A Ƙarƙashin Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar Da Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Katsina, Sanata Yakubu Lado Danmarke Na Jihar Katsina.
Bayanin Hakan Na Kunshe A Cikin Wata Takardar Amincewa Da Naɗin Alhaji Musa Yusuf Gafai A Matsayin Daraktan Tuntuɓa Da Tattara Al’umma Ganin Sun Zaɓi Jam’iyyar PDP A Kowane Matakai.
