Zaharaddeen Ishaq, Fatima Sa’ad @Katsina City News
Alhaji Abdun Malam Babban Dan kasuwa ne Mamallakin Kamfanin AJASCO NIG LTD Yana daga cikin Dilolin da suke samar da Man Fetur a jihar Katsina, ya bayyanawa Jaridar Katsina City News cewa:
“Kamar yadda Gwamnati ke cikin kokarin da kuma wasu tsare tsare da take gudanarwa na ganin ta wadatar da wuraren da ake dauko man Fetur to muna saran kwanannan man zai wadata kuma za’a same shi kasa ga yadda ake saida shi a yanzu.
Bawai Jihar Katsina kadai ke fama da wannan matsalar ta Hauhawar Farashin man Fetur ba idan mukayi duba da sauran jihohi baki daya.
Sannan kuma yan kasuwa masu Gidajen Man su kansu suna bakin kokarinsu wajen ganin ansamu sauki akan farashi to sai dai ya danganta da yadda muke daukoshi daga gurare daban daban.” Yace da ace gwamnati taci gaba da bayar da kudin dauko man Fetur zuwa cikin jahohi da Ansamu sauki sosai to amma ta dakatar kwata kwata, yanzu haka akwai yan kasuwar da suna bin wasu kudade nadaukar man Fetur akalla na shekara guda amma ba abasuba.” Ya bayyana.
A karshe Alh. Abdun Malam ya bayyana cewa da yardar Allah a ta bangaren su ‘Yankasuwar jihar Katsina zasuyi iyakar iyawarsu wajen ganin man ya wadata a jihar Katsina.