Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya INEC ta ce tana da cikakken ƙwarin gwiwa, wajen gudanar da zaɓen a watan da muke ciki.
Yayin da wasu ‘yan ƙasar ke ci gaba da nuna shakku kan ko ƙarancin kuɗin da Najeriya ke fama da shi, zai iya shafar zaɓukan ƙasar da za a fara a watan da muke ciki.
Hukumar zaɓen ta INEC ta ce bayanan da suka samu daga gwamnan babban bankin ƙasar ya ƙara musu ƙarfin guiwar cewar CBN ɗin zai ba su kuɗaɗen da ake buƙata,kafin fara gudanar da zaɓukan ƙasar a makon gobe.
Mai magana da yawun hukumar zaɓen ƙasar, Zainab Aminu ta shaida wa BBC cewa a kwanakin baya shugaban INEC ya ziyarci gwamnan babban bankin ƙasar inda gwamnan ya alƙawarta samar wa hukumarmu kuɗin da za mu gudanar da babban zaɓen ƙasar.
Ta ƙara da cewa mutanen ƙasar ya nawan kambama matsala, a maimakon su jira su ga abin da lokaci zai nuna, tana mai cewa suna fatan samun kuɗin da hukumar za ta gudanar da zaɓen.