Daga Muhammad Kabir
Engr Nura Khalil ya Fadi Hakan ne a wata muhawara da gidan rediyon BBC Hausa ya Shirya ma Yan takarkarun gwamna a jahar katsina ranar Litinin 23/1/2023.
Nura Khalil yace “Muhawarar da Akayi Yau Ya Nuna Abukanan Takarata Basuyi Shirin Mulkin Jahar Katsina Ba”
Dan takarar ya nuna cewa ba yadda za’ayi da Rarar Kudi na Miliyan Dari 2 Zuwa dari da hudu. ya kara da Cewa “Mu a jam’iyyar NNPP munyi tsari wanda Za’a Samar da Kudaden shiga Sama da Biliyan Dari a shekara.
Nura Khalil ya shawarci abukan Takarar sa da su Kuma su rubuta su tsara yadda Zasu Samar da Kudaden shiga, dumin su aywatar da gine ginen da suke so suyi na makarantun da Asibituci, malaman makaranta da sauran su.
Ya kara da cewa “Mu a jam’iyyar NNPP munada tsare-tsare guda goma sha biyar (15) waɗanda Zasu kawoma Jahar Katsina Kudin shiga.