
Fatima Sa’ad @Katsina City News
A ranar lahadi 18/12/2022 Angudanar da taron Mata zalla akar kashin jam’iyar NNPP a Babban ofishin Jam’iyar dake kan Titin Kano cikin garin Katsina.
Shugabar Taron Uwargidan Dantakar Gwamnan Katsina a karkashin Jam’iyyar NNPP Hajiya Farida Barau ta nuna jin dadinta matuka ganin yanda tayi kira kuma aka amsa, Farida tayi kira da gargadi akan matan bisa halin da aka jefasu Sana tayiwa mahalarta taron fatan alkhairi da jajircewa don samun Nasara lnda ta bayya Jam’iyyar ta NNPP a matsayin jaririda da bata da alhakin kowa a tare da ita.
Dantakar Gwamnan na Katsina a Jam’iyyar NNPP ya bayyana takaicinsa bisa ga halin da jam’iyya mai mulki ta jefa al’umma inda yace “yakamata al’umma suyi Allah wadai da ita” yace yakama su Gwamnatin su zagaya wajen al’umma su nemi gafarar su, idan basuyi ba muna fata Allah ya ruguzasu.” injishi a karshe yayi alkawurra da kuma fatan samun Nasara Jam’iyyar NNPP a dukkanin matakai. Tun da farko da yake jawabi a madadin Jam’iyyar NNPP Hon. Liti ‘Yankwani, shugaban na jihar Katsina ya yaba da jajircewa Hajiya Farida inda yayi kira da sauran mata da suyi koyi da irin kokarinta. Kungiyoyin Mata daga kananan hukumomi 34 na jihar Katsina ne suka samu halarta don nuna goyon bayansu a Jam’iyyar ta NNPP mai alamar kayan Marmari.