…Mun gano 30, amma ga 13
Mu’azu Hassan
@Katsina City News
Alhaji Ibrahim Shema, Gwamnan Katsina daga shekarar 2007-2015 yana daga cikin gwamnonin da suka yi mulki cikinsa a da nasara, a lokacin yana Gwamna, Nijeriya ba ta shiga cikin masassarar tattalin arziki ba. Don haka Jihar Katsina ta samu kudi, kuma Shema ya yi amfani da kudin wajen wasu ayyukan cigaba da raya kasa.
Wannan kamar wani alkawari ne ya cika wanda kafin ba shi takara suka yi tare da Gwamnan da ya gada marigayi Malam Umaru Musa ’Yar’adua.
Ruwayoyi masu inganci sun tabbatar cewa, kafin a ba shi takara, sun yi alkawari da Malam Umaru Musa ’Yar’adua cewa zai tabbatar ya kammala duk ayyukan da ya fara, kuma zai dora daga inda ya tsaya na ayyukan cigaba da alheri.
A bisa wannan yarjejeniya aka ba shi takara, kuma Allah ya ba da nasara PDP ta kafa gwamnati har na tsawon shekaru takwas bisa jagorancin Ibrahim Shema.
A zamanin mulkinsa jami’an gwamnatinsa sun rika masa wata irin biyayya, kuma ya rika jan akalar zarensa yadda yake bukata.
Matsalar farko da Shema ya fara samu ita ce, gini bisa tubulin yashi. Yana gaf da barin mulki inda ya fara da kawo wasu dokoki a kan ma’aikata, wanda ya kawo tsarin ajiye aiki ga duk wani Darakta bayan wasu shekaru ko da kuwa shekarun ajiye aikinsa bai yi ba. Da kuma sallamar wasu ma’aikatan da aka dauka aiki sama da dubu biyu, wadanda suka kai kara kotun kula da ma’aikata ta kasa, kuma kotun ta tilasta aka dawo da su bakin aikinsu.
Matsala ta biyu:- Dora dutsin marmara a bisa tubulin na yashi. Duk jami’an da suka yi aiki da Shema, wasu manyan sakatarorin gwamnati ne, wasu kuma daraktoci ne suka ajiye aiki saboda suna son tafiya tare da shi cikin mutunci.
Shema yana da kudin da zai biya su, amma yaki biyansu wata majiya ta ce har Abuja suka bi shi ana sauran awoyi ya bar mulki suna rokonsa ya biya su wadannan kudaden wadanda hakkokinsu ne da suka yi shekaru suna yi wa Jihar Katsina bauta, amma ya tsallake ya bar kasar ba tare da ya cika masu gurinsu ba.
Matsala ta uku:- Wadanda suka yi masa wahalar siyasa suka tsare masa aiki cikin amana lokacin yana mulki cikin barci da saleba, suna dauke bugu ko ta ina. Suka rika tsammanin zai taimaka masu kafin ya bar mulki. Haka suka yi ta jiran gawon shanu har ya bar kasar. Wasu yanzu ko cefanen gida wahala yake masu.
Matsala ta hudu:- Yana tsallakewa, abokai da aminansa suka rika koken ina za su gan shi ya gagara samuwa. Na kusa da shi da yawa da muka yi magana da su sun ce Shema ya watsar da su bayan ya kammala mulki. Ya yanke duk wata hulda da mu’amala da mafi yawan mutanen da suke tare da shi a baya.
Matsala ta biyar:- Rashin kula da wadanda suka sadaukar da ransu a kansa. Binciken marubucin nan ya gano iyalai biyu da suke koke da cewa a kan kare Shema suka rasa ransu, yanzu an yi watsi da su. Da farko akwai tsohon dogarinsa da ya mutu sanadiyar wani hatsari da suka yi a hanyar Daura. Da kuma Malam Halilu Bakori, wanda ya rasa ransa a kan hanyarsa ta dawowa daga bukin gidan Shema.
Matsala ta shida:- Yadda na kusa da shi ke rabuwa da shi dutse a hannun a riga. Marubucin nan ya tara mutane sun kai 30 wadanda ’yan gani-kashe nin Shema ne, amma yanzu ba su ga-maciji da juna.
Matsala ta bakwai:- A shekarar 2019 Shema shi ne ya tarkato Yakubu Lado ya tsaya tsayin daka a kan sai an ba shi takara, kuma aka ba shi, duk da hannunka mai sanda da aka rika yi masa. Yanzu kuma a zaben 2023 yake neman canzawa. Wannan ya jawo masa matsalar da yake ciki a PDP yanzu haka.
Matsala ta takwas:- Lokacin da yana mulki kananan yara sun rika yi masa addu’ar sai ya yi bara. Wanda har in ya biyo hanya yaran su rika fadin “sai ka yi bara!” Ana ganin kamar addu’ar wadannan yaran ta bi shi. Ana zargin yana da kudi, amma ba ya da wadatar zuci.
Matsala ta tara:- Da yadda ake zargin yana takama da ayyukan raya kasa da ya yi kamar da kudin aljihunsa ya yi su, ana ganin kamata ya yi ya dauka cewa alkawari ya yi kafin ya amshi takarar, kuma neman mulkin ya yi. Kudin jama’a ne aka ba shi don ya yi aikin, kuma a lokacin da yana mulkin baki dayan rayuwarsa aka rika daukar nauyi. Don haka takama da wani aiki bai dace ba.
Matsala ta 10:- Ana zargin yana daukar duk wani wanda ya yi aiki karkashinsa, yanzu ya zama mai ’yancin kansa, to ya zama ma ci amana. Wannan ya jawo duk na tare da shi masu ’yancin kansu suka kara nesa da shi suka ’yantar da kansu. Abin da suke fadi shi ne taimakonsa suka yi har ya samu nasarar mulkinsa.
Matsala ta 11:- Bayan ya bar mulki ya yi watsi da lamurran mutanen Katsina, ba zuwa gaisuwa, ba ta’aziyya, ba jaje a kan duk wasu ibtila’o’i daban-daban da suka rika shafar Katsina da jama’arta. Babu inda aka ji muryarsa. An yi ambaliyar ruwa a Jibia, an sace mutane a Kankara, an kashe Eriya Kwamnada na Dutsinma, amma ba ziyara, ba jaje.
Matsala ta 12:- Wasu na zargin kamar alhaki kwaikoyo ne yake bin sa. Domin ana ta takkaddama da muhawarar wacce rawa ya taka lokacin yana Gwamnan Katsina, yayin da Marigayi Umaru Musa ’Yar’adua yana Shugaban Kasa? Lokacin da Marigayi ya kwanta rashin lafiya, kasar an shiga rudu, wacce rawa ya taka a matsayinsa na Gwamnan. A lokacin ya kare martabar ubangidansa?
Matsala ta 13:- Ko Shema ya kwashi kudin gwamnatin Katsina? Wannan kotu ce za ta iya tabbatar da wannan, har kuma ta yi masa hukunci, amma gwamnatin APC sun kafa Kwamitin bincike, wanda aka rika yadawa kai tsaye. A lokacin zaman an yi tonon silili. An rika yi wa juna bankada, wanda Shugaban Kwamitin ya ce ya rage ga kotu ta kammala aikinta.
Hukumar EFCC ta gabatar da Shema a kotuna biyu. Duk ana zaman kotun, kuma ana gabatar da shaidu, suna kuma bayyana abin da suka sani. Bayanan kuma suna da tsoratarwa.
Wadannan sune kadan daga cikin kurakuran da tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema ya aikata da muka hango wasu daga ciki.
Mun yi iyakar kokarinmu don yin magana da tsohon Gwamnan, amma abin ya ci tura. Sai dai mun yi magana da wani makusancinsa baki da baki, sai dai ya kasa samar mana lokaci ko da a waya ne domin Shema ya bayar da amsa.
Abin da ya kamaci tsohon Gwamnan Katsina Ibrahim Shema shi ne gyara kurakuran baya don fuskantar gaba.
Jaridar Taskar Labarai
www.jaridartaskarlabarai.com
Katsina City News
@www.katsinacitynews.com
The Links News
@www.thelinksnews.com
07043777779