Tsohon kyaftin din tawogar ƙwallon ƙafa ta ƙasa, Super Eagles, John Obi Mikel ya sanar da yin ritaya daga buga kwallo bayan ya shafe shekaru 20.
Obi ya bayyana ritayarsa a yau Talata a shafinsa na sada zumunta.
Ya yi ritaya yana da shekaru 35, bayan ya lashe kyautuka da dama ya lashe a ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da kuma Super Eagles, ciki har da gasar cin kofin duniya, da gasar zakarun Turai, da sauransu.
Mikel ya fara ƙwallon ƙafa ne a wata kungiya mai suna Plateau United, kafin ya koma kulob din Lyn Oslo na Norway yana da shekara 17 a shekara ta 2004.
Dan wasan ya koma kungiyar Chelsea ta Ingila cikin wani yanayi mai cike da cece-kuce bayan da Manchester United ta ce ta riga ta saye shi.
Source:
Daily Nigerian Hausa
Via:
Katsina City News