jihar Katsina a Yau
Wasu fitattun mawaƙan Katsina sun ƙaddamar da wata babbar ƙungiyar mawaƙa mai suna ’17+17 PDP Musician Forum Katsina’ a turance, wadda Murtala Madamasi Mani ke jagoranta, an gudanar da taron ƙaddamar da ƙungiyar ne a babbar shalkwstar yaƙin neman zaɓe na PDP dake cikin birnin Katsina, kamar yadda Katsina Online ta rawaito.

A yayin ƙaddamar da ƙungiyar, mawaƙan sun samu baƙuncin Hon. Salisu Yusuf Majigiri, tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a jam’iyyar PDP, tare da wasu manyan baƙi ta ɓangarori da dama, daga ciki har da ‘yan takarar ‘yan majalissu a jam’iyyar PDP.
Hon. Salisu Yusuf Majigiri ya bayyana cewa, “tabbas wannan ƙungiyar ta matasa jajirtattu ne, domin ta daɗe tana mana aiki, amma basu saka mata suna ba sai a wannan lokacin”.

“A zaɓen 2023, tin daga matakin shugaban ƙasa har gwamna, da sanatocinmu 3, da ‘yan majalissunmu 15 a jam’iyyar PDP, da yan majalisu guda 34 na jiha, duk mun yarda da wannan ƙungiya ɗari bisa ɗari”.
“Mun yi alƙawari zamu riƙe amanar wannan ƙungiya ta kowanne mataki da duk abin da suke buƙata, domin duk wanda aka zaɓa ba zamu kasance turin motar wasu ‘yan butulci ba”.

“Zamu rinƙa kiranku duk wasu manyan taruka da zamu rinƙa yi muhimmai, domin ƙungiyarku ita ce gaba-gaba”, inji Majigiri.
Shugaban Ƙungiyar Murtala Badamasi Mani yace, “zamu rinƙa ziyartar gidan gyaran hali, duk wanda aka ɗaure shi a kan bashin kuɗi, tin daga dubu 20 har dubu 30 ga bursunoni 20”.
“Zamu rinƙa ziyartar gidajen marayu domin tallafa musu, da kuma marayun da mazajensu suka mutu suka bar ƙananun yara, kuma zamu ƙara ƙaimi idan muka kafa gwamnati a shekarar 2023”, inji shugaban ƙungiyar.
Bayan kammala taron, sun yi addu’a a kan Allah ya kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabi jihar Katsina, da ma Najeriya baki ɗaya.