Sanata Umaru Al-Makura ya ce Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC za a iya kwatanta shi da shugabannin jamhuriya ta farko irin su Obafemi Awolowo, Nnamdi Azikiwe da Ahmadu Bello Sardauna.
Almakura, tsohon gwamnan Nasarawa, wanda a halin yanzu shi ne Sanata mai wakiltar Nasarawa ta kudu, ya ce Tinubu na matsayi ɗaya da ƴan kishin kasa wadanda su ka taka rawar gani wajen ganin Nijeriya ta samu ƴancin kai.
Da ya ke zanta wa da NAN a yau Litinin, Al-Makura ya ce babu wani daga cikin ƴan takarar shugaban kasa da zai iya kwatankwacin cancanta da nasarorin da jam’iyyar APC ta samu a zaben 2023 kamar Tinubu.
Ya ce haɗakar Tinubu da Kashim Shettima, abokin takararsa zai dora kasar nan kan turbar ci gaba.
“Ba za ku iya samun wani daga cikinsu wanda zai iya kusantar Tinubu da Shettima ba,” in ji shi.
“Ɗauke su ɗaya bayan ɗaya kuma ku kwatanta kowane ɗayan biyun a wasu jam’iyyun, ba za ku yi nisa ba kafin ku gane cewa ba takara ba ce.
“Dauki Tinubu da abin da ya yi a jihar Legas da kasa a zahiri, siyasa, zamantakewa, al’adu da tattalin arziki, ban ga wani dan takarar shugaban kasa da zai yi daidai da cancantarsa da nasarorinsa da hangen nesansa ba.
“A kokarin kare dimokradiyyar Najeriya, Tinubu ya fice daga kasar. Tinubu da sauran su sun tsaya tsayin daka domin tabbatar da cewa dimokuradiyya ta samu gindin zama a kasar nan.
“Jaruman Najeriya nawa ne za su iya yin abin da Tinubu ya yi wa kasar nan tun a 1993? Ya sadaukar da lokacinsa da jin dadinsa don neman dimokuradiyya.
“Don haka kadai, ba shi da wani tamka a tsakanin ‘yan takarar shugaban kasa. A dauki ci gaban ababen more rayuwa da kawo sauyi a Legas.”