Yan Bindiga Sun Shiga Kwalejin Ilimi Ta Isah Kaita Dake Dutsinma, Sun Saci Matan Malami Da Dalibai
Majiyar Funtua Post,Katsina Media Post News Ke Samun Labari A Daren Jiya Talata Wayewar garin Yau
Wasu Ƴan Bindiga Sun Shiga Kwalejin Ilimi ta Isah Kaita College of Education Dake Cikin Garin Dutsinma Jihar Katsina, Inda Suka Yi Awan Gaba Da Wasu Iyalan Malaman Makarantar, Ciki Har Da Wasu Ɗalibai Dake Kwana A Gidajen Malaman.
Kamar Yadda Muka Sami Labari, Daga Cikin Gidajen Da Suka Shiga A Kwalejin har Da
Gidan Dr Ibrahim Babankowa, lnda aka Bayyana Har Sun Tafi Da Matansa Guda Biyu Don Neman A Biya Su KuÉ—in Fansa.
Ko a Satumban bara 2021, yan bindigar sun taba shiga cikin Kwalejin inda har suka saci ya’yan mataimakin shugaban majalisar Isma’il Ado Funtua inda bayan sun yi harbe-harbe suka yi nasarar yin awan gaba da ya’yansa har guda uku.