Sun kwanta barci, ya kalli matarsa ya ce, ko kin san sau nawa Sayyidina Ali ya yi aure?
Matar Ta kalle shi a fusace ta ce, me yasa ba zaka tambaye ni adadin yaƙoƙinsa ba kafin ya yi auran ba!!..?? Saboda Kai matsoraci ne kuma rago ne, ba don Kaka ba Kai ma kasan ba zan auri ragon namiji ba. Ta juya baya.
Mijin Ya ce, Kaico! Ina ma ban tambayeta ba…!!!
Ta juyo ta kalle shi ta sake cewa, me yasa baka bani labarin yadda Sayyidina Ali ya buɗe ƙofar “Kaibar” ba. Kai rannan da na ƙulleka a banɗaki ai kasa buɗewa ka yi…!!!
Ta ja bargo, shi kuma yana jan “Hasbunallahu wa ni’imal wakil”
Ta sake juyowa ta ce, Sayyidina Ali ya kasance yana tsayiwar dare, in yana karatun Ƙur’ani har suma yake yi saboda jin tsoron Allah. Ban taɓa ganinka kana sallar dare ba, sau ɗaya ka taɓa suma, ranar da Ɓera ya shigo mana ɗaki ka kasa fidda shi….!!!!
🥹Kaico, da ban tambayeta ba, da mun yi barci cikin nutsuwa…..!!!! 😂😂😂