Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara ya amsa shan kaye a zaɓen da aka kammala tare kuma da neman afuwa.
Ɗan takarar jam’iyyar PDP Dauda Lawal Dare ne ya kayar da gwamnan.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wani sakon murya da ya fitar ga ƴan jihar, inda ya ce shi da magoya bayansa sun karɓi kaddara.
Ya ce lokacin da gwamnatinsa ta zo kan mulki, ya zauna tare da dukkan masu ruwa da tsaki a jihar wajen ganin an samo hanyoyin dawo da zaman lafiya ta hanyar tattaunawar zaman lafiya, inda ya ce har zuwa yau, babu abin da ya fi addabar jihar kamar rashin tsaro da ake fama da shi.
Matawalle ya ce baya ga tattaunawar zaman lafiya da ƴan bindiga, ya kuma yi aiki tukuru wajen ganin gwamnatinsa ta kawo dukkan ɓangarorin siyasa zuwa karkashin inuwa ɗaya don zaman lafiya da haɗin-kai ya wanzu a faɗin jihar.
Ya ce sun samu nasarar sasanta ɓangarorin siyasa da ba sa ɗasawa, wanda kuma shi ya buɗe hanyar gudanar da yakin neman zaɓe a jihar lami lafiya ba tare da wata matsala ba.