• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Saturday, January 28, 2023
  • Login
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Sashen Hausa

Matar Daraktan SSS ta sa an tsare Abba Gida-gida tare da barazanar kashe hadiminsa a filin jirgin sama a Kano

January 9, 2023
in Sashen Hausa
0
Matar Daraktan SSS ta sa an tsare Abba Gida-gida tare da barazanar kashe hadiminsa a filin jirgin sama a Kano
0
SHARES
22
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Mai ɗakin Darakta-Janar na hukumar jami’an tsaro na farin kaya, SSS, Aisha Yusuf Bichi, ta bada umarnin a tsare ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ta hana shi hawa jirgi da ga Kano zuwa Abuja.

DAILY NIGERIAN ta jiyo cewa dambarwar ta faru ne a kofar shiga ɓangaren matafiya masu alfarma na filin jirgin saman Malam Aminu Kano, yayin da ayarin motocin Yusuf, wanda a ka fi sani da Abba Gida-gida, su ka haifar da cinkoso.

Lamarin ya haifar wa da ayarin motar Aisha Bichi tsaiko, yayin da ta ke shiga ɓangaren domin tashi zuwa Abuja.

Majiyoyi sun shaida wa DAILY NIGERIAN cewa lamarin ya fusata Aisha Bichi, inda dogaranta su ka riƙa duka kan mai uwa da wabi da ababen hawa saboda “raina Hajiya”.

Shaidun gani da ido sun ce da ƙurar ta lafa, sai Abba Gida-gida ya je don ya yi mata ƙorafin abinda dogaranta su ka yi, a matsayin ta na ƙawar mai ɗakin sa, inda ta riƙa yi masa balbalin-bala’i, har ta ke cewa ba za ta bari ya yi gwamna a Kano ba.

Daga nan dai, in ji majiyoyi, sai ga ƙarin jami’an tsaron farin kaya sun zo, inda su ka tsare Abba Gida-gida har sai da Aisha Bichi ta shiga jirgi ta tashi zuwa Abuja.

Wasu majiyoyin ma sun ce kafin ta tashi zuwa Abuja, a lokacin da ta ke ta faɗa, Aisha Bichi ta hango wani hadimin Abba Gida-gida, Garba Kilo yana ɗaukar ta a waya, inda ta sa dogaran ta su “harbe shi kuma ba abin da za a yi.”

“Ta ci gaba da faɗa, ta kuma rantse cewa Abba Gida-gida ba zai shiga jirgi ɗaya da ita ba. Haka dai aka ci gaba da tsare Abba har sai da jirgin ya tashi matar Daraktan,” in ji majiyar.

Share

Related

Source: Daily Nigerian
Via: Katsina City News
Previous Post

“Duk cikin Mutanen Alh. Kabir Masari babu wanda ya taba zuwa har mahaifarsa ya taimake mu sai kai.” Cewar Mutanen kafur ga Aliyu Ilu Barde

Next Post

Dalilin da ya sa na kashe kishiyar mahaifiyata da ɗiyarta -Matashi

Next Post
Dalilin da ya sa na kashe kishiyar mahaifiyata da ɗiyarta -Matashi

Dalilin da ya sa na kashe kishiyar mahaifiyata da ɗiyarta -Matashi

Recent Posts

  • Buhari inaugurates 12 projects in Katsina
  • ZA AYI TAGWAYEN HANYOYI DAGA KOFAR SORO ZUWA KOFAR GUGA
  • PRESS STATEMENT: Old Naira Notes:Kano Govt,Islamic Clerics Calls On Federal Govt To Extend Naira Redesign Deadline
  • Sanarwa! Sanarwa!! Sanarwa!!! Hukumar Sufuri ta KTSTA zataci gaba da amsar tsaffin kudi
  • Dala Inland Dry Port: Kanawa Ga Na Ku
    By Adamu S. Ladan

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In