Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Alh Mannir Yakubu FNIQS ya bude taron kara ma juna sani na kwana ukku ga masu ruwa da tsaki kan harkokin saukaka kasuwanci a Jihar Katsina.
Taron wanda ya gudana a dakin taro na Swiss Continental Hotel dake Kano, Hukumar bunkasa harkokin saka jari ta Jihar Katsina hadin gwuiwa da Majalissar bunkasa harkokin kasuwanci dake a fadar Shugaban Kasa suka shirya taron.
Alhaji Mannir Yakubu ya bayyana cewa, an saukaka harkokin kasuwanci da saka jari a Jihar Katsina fiye da sauran jahohi.
A cewarsa hakan ya biyo bayan wasu sassa a Gwamnatance da Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa domin bunkasa harkokin saka jari, samar lamuni, da kuma tallafama kanana da matsakaitan yan kasuwa.
Kwamishinan Ma’aikatar ciniki da masana’antu na Jihar Katsina Alh. Muntari Kado wanda ya maganta ta bakin Shugaban cibiyar ciniki da masana’antu Engr. Abba Yusuf ya nuna godiyar su ga Gwamnatin Jihar data Tarayya bisa shirya taron.
Daraktan hukumar bunkasa harkokin saka jari ta Jihar Katsina Alh. Ibrahim Tukur Jikamshi ya bayyana bukatar da ake da ita ga mahalartan a wata kasida da ya gabatar. Wadda ya bukaci Mahalarta taron da su dage su dukufa wurin maida hankali da yin aiki tukuru domin ganin haka ta cimma ruwa don tabbatuwar shirin.
A lokacin taron Mr. Ayokunnu Ojeniyi da Jennifer Anya Lekwa daga sashen bunkasa harkokin kasuwanci na fadar Mataimakin Shugaban kasa sun gudanar da kasidu daban daban.
Muhammad Barmo Hadimi Na Musamman ga Mataimakin Gwamna akan Sabbin Kafafen Sadarwa ( New Media ) 31/8/2022