A wata Fira da BBC Hausa tayi da mawakiya kuma ‘yar Film din Hausa Safiyya Yusuf da akafi sani da Safara’u Kwana Casa’in ta bayyana cewa kaso saba’in na mata suna yin bidiyon tsiraicinsu su aje a wayar hannunsu. Don haka ba kanta farau ba, Safiyya da ta canza suna zuwa Safa tace, tayi danasani na fitar Bidiyon tsiraicin nata, wanda hakan ma saida yaja mata kusan watanni uku bata fita, saboda duk lokacin da ta fita sai na zageta ana hantararta wanima sai ya tsina mata.
Safata tace ita wannan lamari kaddara ce, saboda ba ita ta fitar dashi ba, kawai tana zargin kila wani ne zai amshi wayar ya tura batasani ba. Amma ta ce, alokacin da abin ya faru Iyayenta sun mata Uzuri da kwantar mata da hankali akan yarda da Kaddara. Safa tace dayawa mutane suna zarginta da Lesbian amma ba haka bane. Safiyya Yusuf tace tana fatan tazama shararriyar mawakiya irn su, Dabido, da sauran manyan mawakan kudancin Najeriya, kuma ba don komi ba sai dan kishin Arewacin Najeriya, inda zakaga ana daukar mawakin kudanci a bashi kudi yazo Arewa yayi waka, amma mu ba’a gayyatar mu. Injita.