…Illar Ɗan takarar su yafi Illar da Sigari ke yi a jikin Ɗan’adam
Mustapha Muhammad Inuwa, Tsohon Sakataren Gwamnatin APC, a yanzu da ya koma jam’iyyar PDP kuma ya zama Daraktan yaƙin neman zaɓen Atiku da Lado a jihar Katsina, Ya bayyana Ɗan takarar jam’iyyar APC na shugaban ƙasa, a matsayin, mutumin da ba zai amfanawa Arewa komai ba, inda ya bada musalai da cewa; wai yaji ana cewa duk wanda ya zaɓi Tunibu, kamar ya zaɓi Sanata Abu Ibrahim ne saboda tsananin kusanci da shi, yace “Eh munji mun yarda tabbas haka ne, Abu Ibrahim yana da kusanci da Tunibu, amma mi kusancin ya tsinanawa jihar Katsina da Arewa a matsayin Abu Ibrahim na dan Arewa?” Yace Duk Gwamnatin Buhari babu wanda akaiwa gatanci irin gatancin da akaiwa Tunibu, yace ambashi Ministry fiye da Ukku, daga ciki harda ta Ayyuka da Sifiri, yace mi yasa Abu Ibrahim bai amfani da kusancin da ke tsakanin su ya matsawa Tinubu da cewa yaronsa Ministan sufuri da ya maida hankali ya aikin hanyoyin Kano zuwa Katsina da wasu manyan Titunan Arewa ba? Yace “Malam Ummaru Musa ‘Yar’uwa ya gina tashar wutar lantarki mai amfani da iska a Katsina, amma ita wannan Gwamnatin ta gaza idawa, mi yasa Abu Ibrahim baiyi amfani da kusancin da ke tsakaninsu da Tunibu, yace ma yaronsa Ministan wutar lantarki da makamashi Fashola cewa ya maida hankali ya ida Aikin wutar lantarki a Katsina ba?” Yace to ko gado ɗaya suke kwana da Abu Ibrahim da Tunibu ba zamu zaɓeshi ba.
Yace idan ka gangaro nan gida kusa damu, kace zakai tallan Dantakarar su, to Dantakarar su tallan sa daidai yake tallan taba Sigari, “A dokar kungiyar Lafiya ta Duniya, ko wane Kamfanin saida Sigari an wajabta masa cewa dole ya rubuta a jikin kwali”
- taba na haifar da cutar Sankarar Baki
- Taba na haifar da cutar tarin fuka da tarin shika.
- Taba nasa cutar rashin gani
- Taba nasa cutar rashin ji na kunne da sauran cutttukan kunne
- Taba nasawa mutum ciwon zuciya, ciwon hawan jini
- Taba nasa ciwon Sankarar Huhu.
- Taba nasawa a mutu da kuruciya.
To don haka shi wannan Ɗan takarar nasu yama fi Taba Sigari Illa saboda ƙwaƙwalwa ma yake taɓawa. Abubuwan da suke sha ƙwaƙwalwa yake lalatawa. Yace waɗanda basu iya kare kansu da bin Doka da kiyaye wasu abubuwan ɓarna ba, taya zasu iya gyara ɓarna, don haka ku guji waɗannan.” Daka Mustapha Inuwa ya bayyana irin hali da matsalolin da ƙasa take ciki, kuma yayi fatan samun mafita da warwarewar al’amura, kuma ya roƙi da taya addu’a domin nasara ta jam’iyya PDP, kuma yasha Alwashin zasuyi PDP gida-gida da yardar Allah.Mustapha Inuwa ambashi Daraktan yaƙin neman zaɓen Atiku da Lado a jihar Katsina a lokacin da aka bawa Sakataren Jam’iyyar PDP na ƙasa sanata Umar Ibrahim Tsauri Chairman na yaƙin neman zaɓen. An gudanar da taron kaddamar da kwamitin a ranara Lahadi, 20 ga watan Nuwamba a babbar Hedkwatar jam’iyyar PDP ta jihar Katsina dake bisa hanyar kano.