Bayan daukar dogon lokaci batare da masu garkuwa da mutane sun shigo garin dandume ba.
Wayewar garin yau lahadi sun yi dirar mikiya a garin dandume unguwar dajin mare da misalin karfe 1:28pm inda suka shiga gidan sananne mutuminan Alhaji Sani Na Buhari, bayan sun bincika basu ganshi ba suka tafi da iyalansa, matansa da yayansa akalla su 8 suka nausa cikin jeje dasu.
Wato a kalla mutanen nan sun dauki akalla kusan 40min suna dukan kofar bata bude ba, wanda daga baya sukayi anfani da bindiga wajan fasa ginin kamar yanda kuka gani ajikin photo suka shiga, bayan sun shiga kuma suka debi iyalan suka dinga jefusu ta cikin wannan hudar kamar wasu awakai saboda kofar taki budewa.
A cikin wadannan mintunan yaci ace jami’an yan sanda koh sojoji sunyi gaggawar kawo dauki kafin su kaddamar da harin, wanda daga Police Station zuwa inda aka yi fashin akalla 10min zai dau ke ka kafin ka isa.
Jami’an sun iso bayan masu garkuwan sun shiga gidan wanda muna jin irin dauki ba dadin da’akayi dasu wajan hana yan ta’addan daukan iyalan amma hakan bai samu ba.
Allah yakubutar da wadannan bayin Allah daga cikin wannan musiba.
Mun ciro labarin daga shafin Facebook na Asim Suraj Dandume.bayan mun tabbatar da Rahoton.