Gwamnan jihar Katsina Rt Hon Aminu Bello Masari ya nuna damuwa da yadda yan kamfanin wutar lantarki ta KEDCO ke tsawwala biyan kudin wutar lantarki a jihar Katsina.
Gwamnan ya fadi hakan ne a lokacin da sabon shugaban kamfanin Alh Ahmad Dangana ya kai masa ziyara a fadar gidan Gwamnatin jihar Katsina dake nan cikin birnin Katsina.
Gwamna Masari ya kara da cewa a da gwamnatin jihar na biyan kudaden wutar da take sha daga miliyan 35 yanzun ya koma tana biyan miliyan 70
Sabon shugaban ya ziyarci gwamnan ne don gabatar da kansa da kuma jajantawa game da waɗanda harin yan bindiga ya shafa a jihar Katsina.
Source:
Katsina 24