Zaharadeen Ishaq
@ katsina city news
Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Katsina, Alhaji Idris Tune, ya yaba wa
Gwamnatin Aminu Bello Masari saboda irin kokarinta wajen inganta aikin Gwamnati cikin shkearu takwas da suka shige.
Tune, wanda ya yi magana da Jaridar Katsina City News, ta watan Aprilu/ mayu ya zayyano ire-iren sauye-
sauyen da Gwamnatin ta bullo da su da suka sanya aka sami ingantuwar aiki a Jihar.
Ya ce daga ciki akwai biyan albashin ma’aikata cikin lokaci duk da irin kalubalen da ake
fuskanta na karancin kudade a kasar nan.
Idris Tune ya yi bayanin cewa, biyan albashi a kan kari, Gwamna Aminu Bello Masari ya inganta kwazo ma’aikata, tare da ba su karfin giwwar gudanar da aikinsu ba tare da wata matsala ba.
Shugaban ma’aikatan bai tsaya nan ba, sai ya lissafa biyan kudaden fansho da garatuti
ga tsaffin ma’aikata a matsayin daya daga cikin nasarorin Gwamnatin Aminu Bello Masari.
Ya ce, Gwamna Masari ya yi dukkanin mai yiwuwa wajen biyan bashin dukkanin kudaden fansho da ake bin gwamnatin bashi, tare da garatuti, wanda yanzu haka tsaffin ma’aitan na bin bashin na shekaru biyu ne kacal.
Haka ma Tune ya yaba da bullowa da shirin N-Power, wanda ya taimaka matukar
gaske wajen cike gibin da ake samu tsakanin malamai da makarantun Jihar Kastina.
Ya ce, a wannan shirin na N-Power, ya ba da dama ga masu shaidar kammala Digiri, da takardar shaidar malanta ta kasa (NCE), sun sami aikin da za su kula da kansu kafin samun tabbaccen aiki.
Ya ce, a dai wannan shirin na N-Power, sun dauki masu shaidar kammala Digiri su dubu biyu, inda ake ba su Naira dubu 25 duk wata, sai kuma masu NCE da ake ba Naira dubu 20 duk wata, kana an dauki dubu biyar daga cikin su aikin dindindin.
A cewar sa, wannan tsarin ya taimaka ainun wajen samar da aikin yi ga matasa, tare da
yaki da fatara, kuma ya dauke hankalin matasan daga titunan Jihar.
Alhaji Idris Tune ya ce, haka ma Gwamnatin Masari ta ba ma’aikata basukan siyen motoci ko kuma su yi wa motocinsu kwaskwarima domin su iya zuwa wajen aikin cikin sauki.
Ban da wannan ma, sun kuma gabatar da shirin siyarwa ma’aikatan Gwamnati gidajen
da suke cikin zauna muddun na Gwammati ne cikin sauki da rahusa.
Ya ce, wannan shirin ya tallafa wa ma’aikatan Gwamnati da dama sun mallaki gidajen cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.
Alhaji Idris Tune bai tsaya nan ba, ya sake yaba wa Gwamnatin Masari a bangaren kula da kiyon lafiya, wanda hakan ya sa aka fito da shirin Inshorar Lafiya, ta yadda ma’aikata ke zuwa Asibiti ana kula da lafiyarsu cikin sauki da saukakawa.
An buga cikakkiyar hirar a mujjalar katsina city news ta watan Afrilu da Mayu.za a buga saki bidiyon hirar a katsina city news you tube channel a ranar litinin 24/Aprilu.
Katsina city news
@ Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 email: [email protected]